Auto Crash: Yadda mutum 19 suka mutu a Kano

Asalin hoton, Getty Images
Akalla mutum 19 ne suka mutu sannan bakwai sun jikkata a wani hadarin mota da ya faru na ranar Lahadi, a kauyen Dinyar madiga da ke karamar hukumar Takai ta jihar Kano
Wani jami'in hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa reshen jihar ta Kano, Zubairu Mato ya shaida wa BBC cewa hadarin ya hada motoci hudu.
Ya kara da cewa a cikin mutanen da suka mutu 19, 14 maza ne sannan uku mata da kuma yara guda biyu.
Tuni dai jami'an Hukumar Kiyaye Hadurran suka kwashe gawarwakin zuwa asibitin karamar hukumar Takai.
Bayanai sun ce wasu motoci guda biyu da suka yi fakin a bakin hanya ne dai suka haddasa hadarin.
Ana dai samun yawaitar hadurra a kan titunan Najeriya da ke haddasa rasa daruruwan rayukan 'yan kasar.
Wasu na danganta irin wadannan hadurra da rashin kyawun titunan kasar da kuma irin tukin gangaci da wasu direbobi ke yi.







