Labaran Abubuwan da ke faruwa a Najeriya 08/07/2019: Kotu ta bayar da belin Sanata Abbo

Ku kasance da mu domin kawo muku batutuwan da ke faruwa a Najeriya da kasashe makwabta.

Elisha Abbo

Asalin hoton, Elisha Abbo

Bayanan hoto, Sanata Elisha Abbo ya ce an goge bangaren da matar ita ma ta buge shi

1- Babbar Majistare da ke Zuba a Abuja ta amince da bayar da belin Sanata Elisha Abbo a kan kudi naira miliyan biyar, 'yan awanni bayan da 'yan sanda suka gurfanar da shi bisa tuhume-tuhume guda biyu na cin zarafi.

Kotun ta kuma ce dole ne sanatan ya mika sunan mutum biyu da za su tsaya masa.

Shi dai sanata Abbo ya ki amince wa da laifuka biyun da ake tuhumar sa da su.

Wani bidiyo ne dai ya bayyana sanatan yana dukan wata mai tsaron shagon kayan jima'i.

Sanata Elisha Abbo ya shaida wa BBC cewa shi ne a cikin bidiyon da aka yi ta bazawa amma kuma ya ce an goge bangaren da matar ita ma take bugun sa.

Kwamishinan 'yan sandan birnin Abuja, Bala Ciroma ya shaida wa BBC cewa an gurfanar da sanatan amma kuma bai fadi abubuwan da ake tuhumar sanatan da su ba.

Jaridar Intanet ta Premium Times, wadda ta fara sakin bidiyon, ta rawaito mai magana da yawun 'yan sanda, Anjuguri Manzah, cewa "'yan sanda sun shigar da shari'a ne bayan sun ga irin halayyar sanatan a bidiyon".

A ranar Larabar da ta gabata ne sanata Abbo ya yi kuka tare da neman afuwa kan abin da ya aikata, a wani taron manema labarai, kwana guda bayan da 'yan sanda suka ce sun fara bincike.

Wannan layi ne

2- Injiniya Buba Galadima wanda shi ne shugaban tsagin jam'iyyar APC da ake kira rAPC ya bayyana a kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa domin ba da shaida, a ranar Litinin.

Buba Galadima kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito ya ce har yanzu shi dan jam'iyyar APC mai mulki ne, sai dai ya ce jam'iyyar tasa ta rAPC ta yi hadin gwiwa da jam'iyyar adawa ta PDP da dan takararta ne domin samar da shugaba mai ilimi da tsoron Allah da kuma nagarta.

Injiniya Buba wanda ya yi ikrarin ya san Shugaba Muhammadu Buhari tun shekarun 1960 kuma ya yi aiki da shi tun lokacin da ya fara neman takarar shugaban kasa a 2003, ya ce sun raba gari saboda ya gaza cika alkawuran da ya daukar wa 'yan Najeriya.

Da lauyan Shugaba Buhari, Wole Olanipekun yake yi masa tambayoyi kan ko yana sane da kasancewar 'yarsa a cikin gwamnatin Buhari, sai Buba Galadima ya ce 'yar tasa ta taimaka wajen hawan Buhari mulki.

Ya kuma kara da cewa "Ina son fadin cewa 'yata na daya daga cikin mutanen da suka fi cancanta a gwamnatin nan. Digirinta na farko guda biyu, tana da digiri na biyu guda uku kuma tana yin na hudu."

Buba Galadima

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Buba Galadima na da tsohuwar alaka da Muhammadu Buhari
Wannan layi ne

3- Rahotanni daga Katsina na cewa wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu satar mutane ne sun far wa wasu kauyuka guda uku a jihar inda suka shiga suna kabbara.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, sun yi musayar wuta da maharan.

Maharan dai sun shiga kauyukan Makera da Dan Sabau da Pawwa da ke yankin karamar hukumar Kankara.

Bayanai sun ce 'yan bindigar wadanda suka shiga garuruwan a kan babura sun yi amfani da bindigogi da gurneti, inda aka ce sun kashe mutum shida.

Wannan layi ne

4-A ranar Litinin din nan ne sabon shugaban kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari yake fara aiki bayan da tsohon shugaban kamfanin, Maikanti Baru ya yi masa handi-oba.

A ranar 20 ga watan Yunin 2019 neShugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Mele Kolo Kyari a matsayin sabon shugaban kamfanin man na, NNPC.

Mele Kyari

Asalin hoton, NNPC TWITTER

Bayanan hoto, Mele Kyari gogaggen ma'aikaci ne