Zaben 2019: Buhari ya mayar da martani kan rahoton EU

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta ce tana maraba da rahoton da Tarayyar Turai ta fitar kan zaben 2019 da aka yi a kasar.

Mai magana da yawun Shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya bayyana haka a wasu jerin sakwanni da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ce gwamnatin ta yi alkawarin duba rahoton dalla-dalla sannan za ta yi aiki da shawarwarin da rahoton ya kunsa.

Malam Garba Shehu ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta jajirce wajen tabbatar da tsarin damokradiyya mai tsafta shi ya sa ta goyi bayan gayyatar da hukumar INEC ta yi wa masu sa idon na Tarayyar Turai.

Ya ce gwamnatin za ta tabbatar da cewa an gyara duk wasu kura-kurai a zabe na gaba ta hanyar hada kai da duk 'yan kasar da hukumomi da jam'iyyu da kungiyoyin farar hula da kafofin yada labarai da sauran masana wajen ganin an gyara nakasun da ke tattare da tsarin zaben Najeriyar kamar yadda EU din ta bayyana.

Ya ce gwamnati ta yi amannar cewa hukumar INEC ta gudanar da sahihin zabe kuma za ta ci gaba da gyara kura-kuranta na baya.

Mai magana da yawun Shugaban ya ce gwamnati ta yi takaicin tashe-tashen hankali da aka yi a wasu bangarorin kasar, kamar yadda rahoton EU din ya nuna, sai dai gwamnati ba ta ganin rikice-rikicen sun yi tasiri a sakamakon zaben.

Ya kuma ce wannan wata shaida ce da ke nuna cewa zaben ya bayyana bukatar 'yan Najeriya, kuma sauran kasashen duniya na Shugaba Muhammadu Buhari dari bisa dari a zaben sa da aka yi a karo na biyu.

Short presentational grey line

Me rahoton EU din ya ce?

Tawagar Tarayyar Turai a zaben Najeriya

Asalin hoton, @inecnigeria

Tawagar Tarayyar Turai da ta sa ido a zaben Najeriya ta ce akwai bukatar a sauya tsarin zaben kasar bayan gano wasu matsaloli a zabukan 2019 da aka gudanar.

Tawagar ta Tarayyar Turai ta fadi haka ne lokacin da take gabatar da rahotonta na karshe kan zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisa da gwamnoni da aka gudanar a 2019.

Babbar jami'ar da ta jagoranci tawagar Maria Arena ta ce an lalata gaskiyar tsarin zaben Najeriya na 2019 saboda rikici da tsoratarwa.

Ta ce an samu matsaloli da suka shafi tsaro da matsalar kai kayan zabe da kuma rashin fitowar jama'a.

Daga cikin shawarwarin da rahoton ya bayar, sun hada da inganta tsarin tattara sakamakon zabe, musamman tsarin da zai bayyanawa jama'a sakamakon kafin sanar da shi.

Rahoton na zuwa bayan watanni uku da aka gudanar da zaben shugaban kasa wanda shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya lashe.

Tarayyar Turai ta dora laifin matsalolin da aka samu akan jam'iyya mai mulki, kan rashin tsawatarwa ga magoya bayanta da rashin daukar matakan kaucewa cin karo da matsalolin.

Ta ce an yi amfani da karfin mulki a bangarorin Tarayya da jiha.

Kuma dakatarwar da aka yi wa Alkalin alkalan kasar, makwani kafin a gudanar da zabe ya saba wa 'yancin shari'a a Najeriya.

Dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar ya shigar da kara kotu inda yake kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa.

Tarayyar Turai ta bukaci a gaggauta sauya tsarin zaben Najeriya saboda matsalolin da ta gano kafin zaben 2023.