Yaushe Buhari zai nada sabbin ministoci?

Asalin hoton, Facebook/Nigerian Presidency
- Marubuci, Awwal Ahmad Janyau
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
Batun nadin sabbin ministoci a Najeriya na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce bayan rantsar da sabuwar gwamnati.
A ranar 29 ga Mayu aka sake rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a wa'adin shugabanci na biyu.
Kuma sama da mako biyu kenan aka shafe ba tare da shugaban ya sanar da sabbin ministocinsa ba da za su ja ragamar gwamnatinsa.
Fadar shugaban kasar ta fito ta karyata wasu jerin sunaye da aka dinga yadawa a kafafen sadarwa na Intanet cewa su ne sabbin ministocin Buhari.
A wa'adin mulkinsa na farko, shugaban bai nada ministoci ba sai bayan kusan watanni shida da karbar ragamar mulkin kasar.
Yadda 'yan kasar suka kwashe tsawon lokaci suna jira Shugaba Buhari ya bayyana ministocinsa a farkon mulkinsa, suna fatan a wannan karon ba zai yi jinkiri ba domin ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.
Bayan zaben shugabannin sabuwar majalisa, ana tunanin shugaban ya tura sunayen ministocinsa domin fara tantance su. Sai dai ba a san lokacin da za a dauka ba.
Buhari zai zarce da ministocinsa ne?
Wasu na ganin akwai yiyuwar shugaba Buhari zai tafi da wasu daga cikin ministocinsa da ya fara aiki da su a wa'adinsa na farko, musamman yadda ya dinga yaba wa ayyukansu.
A taron majalisar Ministocin na karshe kafin karewar wa'adin farko, Shugaba Buhari ya ce irin rawar da ministocin suka taka ne dalilin da ya sa ya ci gaba da tafiya da su har tsawon shekara uku da rabi wato zuwa karshen wa'adinsa ba tare da ya sauya su ba.
Sai dai kuma wasu na ganin kalaman shugaban sun nuna alamun zai iya ci gaba da aiki da yawancin ministocin da suke ganin ba rawar da suka taka, kuma babu tabbas ko zai yi sabon zubi.
Wasu 'yan Najeriya dai na ganin ya kamata shugaban ya zubar da ministocin ya dauko sabbi, yayin da kuma wasu ke ganin akwai daga cikin ministocin da ya kamata a ci gaba da aiki tare da su, kamar yadda wasunsu suka tafka muhawara a shafin Facebook na BBC.


Daga cikin minitocin da ake ganin Buhari zai zarce da su sun hada da ministan ma'aikatar makamashi da ayyuka da samar da gidaje, tsohon gwamnan Lagos Babatunde Fashola.
Sai ministan sufuri Rotimi Ameachi da Hadi Sirika na sufurin jiragen sama da ministan kwadago Chris Ngige da ministan cikin gida Janar Danbazau da ministan Lafiya Isaac Adewole.
Sharhin Dakta Abubakar Kari
Dakta Abubakar Kari, mai sharhi kan lamuran yau da kullum a Najeriya ya shaida wa BBC cewa "babu tabbas ko shugaban zai bar wasu ko ma ya bar da dama daga cikinsu."
"Idan har kana tare da mutum kuma ka dinga yaba shi, to ba mamaki ci gaba da tafiya da shi kake son yi," in ji Kari
Ya kara da cewa tun tuni ya kamata a ce shugaban ya canza ministocinsa saboda "ba wata rawa da suka taka ko ci gaba da suka kawo ga ci gaban kasa."
Dakta Kari ya bayyana cewa akwai ministoci da dama da ba su taka rawar gani ba, kuma idan har shugaban zai ci gaba da aiki da wasu ministocin, "to ba su cancanta ba."
"Idan ka yi maganar ma'aikatu kamar na lafiya da sadarwa da na jiragen sama, ayyukan da ministocin suka yi bai gamsar da 'yan Najeriya ba."
"Sun kuma yi alkawura da dama kamar na magance matsalar wuta da kuma hanyoyi da suka kasa aiwatarwa," a cewarsa.
Dakta Kari ya jaddada cewa wadannan abubuwan da ya lissafo, ba wai yana nufin cewa ba su tabuka komai ba, "mutane dai ba su ga ayyukan da suka yi tunanin za a yi ba."
Har yanzu babu wani takamaiman jawabi ko bayani da ya nuna cewa tabbas zai kara tafiya da su, ko kuma a'a.
A cikin jawabin karshe ga ministocinsa, Buhari ya yi ikirarin cewa sun samu nasarar cika alkawuran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe, kuma ministocin sun taka rawa ga samun nasarar.
Masana harkokin tsaro da dama irinsu Malam Kabiru Adamu sun amince cewa shugaban ya samu gagarumar nasara a fannin tsaro - musamman a yaki da kungiyar Boko Haram wacce ta kashe dubban mutane sannan ta raba miliyoyi daga gidajensu.
Sai dai sun nuna gazawar shugaban wajen shawo kan matsalolin 'yan bindiga da masu satar mutane don karbar kudin fansa a jihohin arewa maso yammaci, matsalolin da suka yi kamari a yanzu.











