2019: Wanne darasi muka koya daga zaben Najeriya?

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Tomi Oladipo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja
An sake zabar Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a karo na biyu kan wa'adin shakara hudu.
Babban abokin hamayyarsa a takarar Atiku Abubakar, ya ce zaben "ba na gaskiya" ba ne ya kuma sha alwashin shiga kotu.
Ga dai wasu abubuwa biyar da muka koya daga zaben mai cike da ce-ce-ku-ce.
1. Ya kafa tarihi - saboda dalilan da ba daidai ba
Ya kamata wannan zaben da ya zama mafi girman da ba a taba irinsa ba a nahiyar Afirka, ganin cewa wajen mutum miliyan 84 ne suka yi rijista - amma sai ga shi kashi daya bisa uku ne kawai daga cikin masu rijistar suka fita zabe.
Don haka abun da aka yi tsammani cewa zai kafa tarihi, ya kafa din amma kuma kan wani dalilin na daban ba na yawan masu kada kuri'a ba
Zaben 2019 shi ne wanda mutane ba su fita kada kuri'a sosai ba a tarihin siyasar kasar cikin shekara 20.
Tun shekarar 2003 ake samun raguwar masu kada kuri'a a kasar. Raguwar masu kada kuri'ar - musamman daga kudancin kasar na nuna yadda mutane ke dawowa daga rakiyar al'amuran siyasa da yin amanna kan abun da za su mora a jikinta
Yawan mutanen da ke fitowa kada kuri'a a fadin kasar na raguwa tun 2003. Raguwar - musamman a kudancin kasar - yana nuna dawowa daga rakiyar siyasar kasar da kuma abin da za ta iya yi wa mutanen.



2. Har yanzu ana ji da Buhari a arewa
Babban abokin hamayya Atiku Abubakar ya ce an yi magudi wajen tattara kuri'u.
Ya ce abun mamaki ne a ce gaba daya kuri'un da aka kada a daya daga cikin wuraren da yake da karbuwa, Akwa-Ibom, ya ragu da kashi 50 cikin 100 a wannan zaben fiye da a 2015.
Buhari na da goyon baya sosai a arewacin kasar, inda ake masa kallon mutum mai akida kuma mai kaunar talakawa. Soyayyar da ake nuna masa ba ta taba raguwa ba a zabuka biyar din da suka wuce.
Mutane da dama ba su fito ba a yankunan kudancin Najeriya, inda Atiku ya yi fatan zai samu kuri'u sosai.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya yi maganar yawan mutanen da suka fito kada kuri'a wanda ya kasance kashi 29 cikin 100.
Atiku Abubakar ya ce a zaben 2015 mutanen da suka fito sun fi haka yawa kuma ya ayyana cewa ba komai ya jawo haka ba sai toshe wa masu kada kuri'a damarsu.
Sai dai duk da haka, ya ci a kudanci, amma bai samu yawan kuri'un da za su sa ya kamo kuri'u miliyan 4 da Buhari ya samu ba.



3. Matsalar tsaro ba ta hana magoya bayan Buhari fitowa ba
Haka zalika, Atiku Abubakar ya bukaci ya san dalilin da ya sa mutane da dama suka fito yin zabe a yankunan da Boko Haram ya daidaita a arewacin Najeriya.
Jam'iyyar APC mai mulki na da karbuwa sosai a Jihohin Barno da Yobe a arewa maso gabas. Goyon bayan da take da shi bai ragu ba, duk da matsalar tsaron da ya raba mutane miliyan biyu da gidajensu.
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta tsara yadda mutane 400,000 da rikicin ya raba da gidajensu za su yi zabe a sansanonin 'yan gudun hijirar da suke.
Mutane da dama daga yankin sun fito sun yi zabe duk da hare-hare da kungiyar Boko haram da reshenta na ISWAP suka kai a ranar.

Asalin hoton, AFP
Sai dai rikici ya barke a wasu sassan kudancin kasar ciki har da jihar Rivers, don haka ba a yi zabe a kananan hukumomi biyu ba kuma babu mamaki rikicin ya shafi fitowar mutane a duka jihar, a cewar Idayat Hassan ta Cibiyar samar da ci gaban Demokradiyya a Abuja.

4. Tsaikon ya shafi 'yan takarar biyu
INEC ta dage ranar zaben da mako guda saboda wasu matsalolin kayan aiki.
Wannan ya jawo korafe-korafe daga mutanen da suka riga suka tafi garuruwansu don kada kuri'a.
Sai dai wannan ya shafi magoya bayan duka 'yan takarar biyu.
5. Zabe da na'urar card reader ya fi zama sahihi
Wasu masharhanta na ganin cewa amfani da na'urar tantance masu kada kuri'a zai sa yin magudi ya yi wahala.
Duk da cewa an samu na'urorin da suka yi gardama, wasu na ganin cewa amfani da fasaha ya taimaka wajen fahimtar halayyar masu zabe a rumfunan zabe da kuma kawar da magudi a lokacin zaben.











