Masu neman mukami ne ke zanga-zanga - Buhari

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, A karshen watan Mayu ne aka sake rantsar da shugaban a karo na biyu

Fadar shugaban Najeriya ta yi watsi da korafe-korafen wasu 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulkin kasar da ke adawa da ci gaba da tafiya da wasu na kusa da Shugaba Muhammadu Buhari.

A ranar Litinin ne wasu 'yan APC suka gudanar da zanga-zanga a Abuja, domin neman shugaban da ka da ya sake nada ministocin da suka ce sun "hana ruwa gudu a wa'adinsa na farko, saboda ba sa son talaka, kuma ba su da gaskiya".

Sai dai mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, ya gayawa BBC cewa wasu masu neman mukami ne suka debo mutane domin yin zanga-zangar.

"Wasu sun sa ido kan wadannan mukamai saboda wasu bukatu nasu," in ji shi.

Har yanzu dai ana dakon sunayen mutanen da shugaban, wanda aka rantsar karo na biyu a watan Mayu, zai gabatar domin nadawa a matsayin ministocinsa.

Masu zanga-zangar sun nuna fargaba ne kan yiyuwar Buhari zai iya sake tafiya da mutanen da suke zargi a wa'adin mulkinsa na biyu.

Sai dai Malam Garba Shehu ya ce "Idan mutum ba da shi ake tafiyar gwamnati ba, to ba abin da zai gamsar da shi."

Ya kara da cewa ba yau aka fara irin wannan zanga-zanga ta masu neman bukata ba don suna neman a cire wani ko a nada wani don a biya bukatunsu.

Kuma masu zanga-zangar sun ce matukar aka sake nada irin wadannan mutanen a mukamai na siyasa to kuwa za su raba-gari da duk wasu abubuwa da suka shafi jam'iyyar ta APC.

Da dama daga cikin 'yan kasar da ma wasu magoya bayansa na alakanta tafiyar hawainiyar da suka ce gwamnatinsa na yi da rashin zabar mutanen da suka cancanta a matsayin ministoci da sauran shugabannin muhimman ma'aikatun gwamnati.

Haka kuma ana fargabar ka da a sake shafe dogon lokaci kafin a nada ministocin kamar yadda ya yi a 2015, lamarin da masana suka ce ya kawo tsaiko a harkokin mulki.

Amma Garba Shehu ya alakanta tsaikon da aka samu da hutun da majalisa ta tafi, inda ba za ta dawo ba sai a watan Yuli.

"A bari sai majalisa ta dawo an ga ba a yi nade-naden ba sannan a yi korafi, amma ba wani saba doka da tsarin mulki da aka yi ta bagaren sha'anin nade-nade," in ji shi.

Wadannan korafe-korafe na zuwa ne a daidai lokacin da wasu matasan jam'iyyar suka tilastawa shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan sauya wasu mutane da ya nada domin taimaka masa, bayan da suka zarge su da kasancewa masu adawa da gwamnati da kuma jam'iyyar tasu.