Kalli hotunan yadda aka yi jana'izar Mohammed Morsi

An binne zababben shugaban kasar Masar na farko, Mohammed Morsi, wanda sojoji suka hambarar da gwamnatinsa a shekarar 2013.

An rufe marigayin a makabartar Al-Wafaa Wa al-Amal da ke gabashin birnin Alkahira ranar Talata.

Lauyansa ya shaida wa kamafnin dillancin labarai na AFP cewa an binne shi ne a birnin Alkahira ranar Talata da safe a gaban iyalansa.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya yi mutuwar shahada.

Hakazalika an yi wa marigayin sallar jana'iza a birnin Ankara na kasar Turkiyya a ranar Talata.

Har ila yau an yi masa sallah a masallacin Dergah na birnin Sanlıurfa a kasar ta Turkiyya.