Kamfanin Huawei ya ce Amurka na kawo masa wargi

Asalin hoton, Getty Images
Mamallakin kamfanin kera wayar hannu na Huawei Ren Zhengfei ya tsaya kai-da-fata cewa Amurka na kawo wa kamfanin wargi ne kawai.
Yayin da yake magana da kafar yada labarai mallakin kasar China, Mista Ren ya rage kaifin rikicin, inda ya ce babu wanda zai iya ja da kamfanin wajen samar da fasahar layin salula na 5G.
Makon da ya gabata ne Amurka ta saka Huawei a jerin kamfanonin da za ta yanke huldar kasuwanci da su har sai sun samu lasisi.
"Abin da 'yan siyasar Amurka ke aikatawa wargi ne kawai a gare mu," in ji Ren, a ta bakin kafar yada labaran China.
Huawei na fuskantar matsi daga kasashen turawan Yamma karkashin jagorancin Amurka game da hadarin da ke akwai idan aka yi amfani da fasahar kamfanin ta 5G.
Hukuncin Amurka na dakatar da kamfanin ya fara haifar da sakamako a ranar Litinin bayan da Google ya dakatar da Huawei daga samun sababbin manhajojinsa a kan samfurin Android.
Jim kadan bayan haka a Litinin din ma'aikatar kasuwancin Amurka ta bai wa kamfanin lasisin wucin-gadi, wanda zai taimaka wa kamfanin ci gaba da huldar kasuwanci.
Amurka ta ce za ta bayar da lasisi "wanda zai bai wa masu amfani da wayoyin kamfanin damar ci gaba da amfani da su da kuma layukan sadarwar broadband a kauyuka", in ji sakataren kasuwanci Wilbur Ross.
Cibiyar kula da tsaron Intanet ta Birtaniya ta wallafa shawarwari ga masu amfani da wayoyin Huawei a shafinsa na Intanet.
Kamfanin Huawei ya dade a tsaka-mai-wuya bisa rikicin tattalin arziki tsakanin Amurka da China.
Masu amfani da wayoyin kamfanin dai na cikin zullumin abin da ka iya faruwa da su, yayin da kuma tasirin abin mai yiwuwa ne ya zama mai girman gaske ga kamfanin kansa.











