Kirkirar masarautu: Abin da ya sa Hakimin Bebeji yin Murabus

Ana cigaba da samu sabbin bayanai kan kirkirar masarautu a Kano

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana ci gaba da samu sabbin bayanai kan kirkirar masarautu a Kano

Hakimin karamar hukumar Bebeji kuma Dan Galadiman Kano, Haruna Sanusi ya yi murabus.

Dan Galadiman ya bayyana matsalar rashin lafiyarsa da kuma sauyin da aka samu na kacaccala tsarin masarautar Kano a matsayin dalilansa na Murabus.

Dan Galadiman ya sanar da murabus din a wata wasika da ya aike wa sakataren gwamnatin jihar Kano dauke da sa hannunsa.

Bebeji ta fada ne karkashin masarautar Rano a yanzu, bayan rarraba masauratar Kano da aka yi a makon da ya gabata.

Murabus din hakimin na zuwa ne adaidai lokacin da al'umnar karamar hukumar wudil suka bayyana cewa ba za su amince da zamansu a karkashin masarautar Gaya ba.

Wasikar murabus din hakimin Bebeji

Asalin hoton, Bebeji Emirate

Bayanan hoto, Wannan ita ce wasikar murabus din da Hakimin Bebeji ya aika wa gwamnatin jihar Kano

A ranar 8 ga watan Mayu ne dai gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiri sababbin masarautu hudu masu daraja ta daya, wanda ake zargin ya yi hakan ne da niyyar karya tasiri Sarkin Sunusi na II.

Sarakunan da aka nada sun hada da Alhaji Aminu Ado Bayero wanda shi zai jagoranci masarautar Bichi, da kuma Dakta Ibrahim Abubakar a matsayin sarkin Karaye, sai Tafida Abubakar Ila a matsayin sarkin Rano da kuma Alhaji Ibrahim Abdulkadir a matsayin sarkin Gaya.

Masana tarihi dai kamar Dokta Tijjani Naniya na gani cewa kirkirar wadanan masarautu zai rusa tarihi da darajar da aka san masarautar Kano da ita sama da shekaru 2000.

Sabbin Masarautun Kano

Dokta Naniya, ya ce "duk da cewa ana maganar 'yanci ai ita ma majalisa jama'a ne suka zabe ta, kuma ta san nauyinta shi ne ta kare mutunci da martaba da tarihi da al'adar mutane."

"Al'ada ce ke bambanta mutumin Kano da Katsina da yadda tsarin sarautar take, hakazalika ita ke bambanta mutumin Kano da na Borno, bambancin tsarin rayuwa da masarauta da kuma yadda tsarin zamantakewar jam'a take."

Ya ce inda a ce maganar nan tasowa ta yi daga masarautu ko kuma jama'ar yankunan suna korafin cewa masarautar Kano tana yi musu wani abu da ba daidai ba, kuma suka nuna cewa dama a tarihi suna da 'yancin irin wannan sai a duba kokensu.

Muhammadu Sanusi na II

Asalin hoton, KANO

A ranar Asabar wasu matasa maza da mata suka shirya wata zanga zanga domin nuna rashin goyon baya kan kirkiro wasu sabbin masarautu a Kano, karkshin kungiyar ''Kano First.''

To amma hakan bai yi wu ba sakamakon wasu da ake zargin 'yan daba ne suka mamaye gurin tun da sanyin safiya dauke da manyan hotunan Sabon Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero da na Marigayi Sarki Ado Bayero.

Masu zanga-zanga

Masarautar Kano ita ce masarauta mafi girma a Najeriya mai kananan hukumomi 44 a karkashinta.

Sai da a yanzu haka sarkin an bar shi da kashi daya cikin biyar na yankunan da yake da iko da su.

Har yanzu sarkin na Kano Muhammadu Sanusi II, wanda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ne bai ce komai ba kan wannan lamarin.

Gwamnatin Jihar Kanon dai ta dage a kan cewa ta kirkiri sabbin masarautun ne domin ci gaban al'umma.

Yadda tsarin masarautun zai kasance

Sarkin birni da kewaye na da kananan hukumomi 10 a karkashinsa da suka hada da:

  • Fagge
  • Nassarawa
  • Gwale
  • Dala
  • Tarauni
  • Kano Municipal
  • Minjibir
  • Ungogo
  • Kumbotso
  • Dawakin Kudu

Sarkin Rano kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:

  • Rano
  • Bunkure
  • Takai
  • Kibiya
  • Sumaila
  • Doguwa
  • Kiru
  • Bebeji
  • Kura

Sarkin Gaya kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:

  • Gaya
  • Ajingi
  • Albasu
  • Wudil
  • Garko
  • Warawa
  • Gezawa
  • Gabasawa

Sarkin Bichi kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:

  • Bichi
  • Bagwai
  • Shanono
  • Tsanyawa
  • Kunci
  • Makoda
  • Danbatta
  • Dawakin Tofa
  • Tofa

Sarkin Karaye kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:

  • Karaye
  • Rogo
  • Gwarzo
  • Madobi
  • Rimin Gado
  • Garun Malam

Wata sanarwa da gwamnatin jihar Kano ta fitar ta ce Sarkin Birnin Kano da Kewaye Muhammadu Sanusi II shi ne zai samu Shugaban majalisar zartarwa na Masarautun guda biyar, sannan kuma Sarkin Rano shi zai zama mataimakinsa.

Sannan shugabancin wannan majalisa zai zama na karba-karba ne inda kowane shugaba zai shekara biyu, inda bayan kammaluwar wa'adinsa sai kuma gwamnatin jiha na da hurumin kara masa wani wa'adin karo na biyu.Sannan sauran 'yan majalisar masarautun sun hada da:

  • Sakataren gwamnatin jiha
  • Kwamishinan kananan hukumomi
  • Shugabannin kananan hukumomi
  • Hakimai masu nada sarki bibbiyu daga kowace masarauta
  • Wakilcin mutum biyar da gwamna zai nada.

Sanarwar ta kuma ce: "Sako na karshe kuma shi ne sabuwar dokar bata hana wani wanda ya gaji sarautar Kano daga sauran sababbin masarautun guda hudu zama Sarkin Birnin Kano da Kewaye ba, in dai har sun gada."