Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kano: Abin da ya sa 'yan majalisa suka yi wa kansu dokar yanke talauci
Kakakin majalisar dokokin jihar Kano Kabiru Alhassan Rurum, ya ce sabuwar dokar da suka gabatar ta bai wa shugaban majalisa da mataimakinsa fansho na har abada za ta taimaka wajen ragewa 'yan siyasa da suka sauka daga mukamansu radadin wahala.
Majalisar dokokin jihar ta gabatar da sabon kudurin dokar ne a ranar Talata, wanda zai bai wa kakakin majalisar da mataimakinsa fansho tsawon rayuwarsu da kuma zuwa kasashen waje duba lafiyarsu duk shekara.
Rurum ya shaida wa BBC cewa an yi sabuwar dokar ne "don a rage cin hanci da rashawa da kuma hana 'yan siyasa shan wahala a yayin da ba sa kan mukamai."
Wannan doka dai na shan suka sosai ganin yadda talauci ya yi wa mutanen kasar katutu. Kuma ita ce doka ta biyu da majalisar ta gabatar a wannan makon da suka jawo ce-ce-ku-ce.
Baya ga ba su fansho na har abada, sabuwar dokar za kuma ta ba su damar mallakar sabbin motoci duk bayan shekara hudu.
Sannan za su samu damar zuwa kasashen waje domin duba lafiyarsu, ko kuma duk asibitin da ya yi musu a fadin Najeriya tsawon rayuwarsu.
Sai dai ba a san adadin yawan kudin fanshon da za su dinga karba ba, amma idan har gwamnan jihar ya amince da dokar, to Kano za ta zamo jiha ta farko da za ta fara amfani da irin wannan dokar.
Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da ke fama da matsanancin talauci a duniya, kuma Kano ce jihar da ta fi yawan al'umma.
Ce-ce-ku-ce
Mutane da dama na jihar Kano da ma sauran sassan Najeriya na ta tofa tasu kan wannan lamari, musamman a shafukan sada zumunta da muhawara.
Da yawan jama'a na ganin akwai abin da talakawan jihar Kano suka fi bukata fiye da wannan dokar, da suke ganin tamkar "ta yankewa 'yan siyasar talauci ne na har abada."
Ga abun da wasu ke cewa:
Sunusi Musa wani lauya ne dan jihar Kano, kuma a shafinsa na Twitter ya ce: "Wannan dokar ta bai wa shugabannin majalisar fansho tsawon rayuwarsu abu ne da ya kamata dukkanmu mu yake ta."
Shi ma Nafi'u T ya rubuta a Twitter cewa: Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Kano da mataimakinsa sun yi wa kansu dokar samun fansho na har abada da zuwa kasashen waje don duba lafiyarsu.
Wadannan ne dai mutanen da suka nemi Ganduje ya binciki masarutar Kano."
Cin gajiyar fansho har bayan rai
A yanzu haka dai tsofaffin shugabannin Najeriya da gwamnonin jihohi da shugabannin majalisun dattawa da na wakilai suna karbar fansho bayan sun sauka daga mulki.
Kungiyar Transparency International ta ayyana Najeriya a matsayin kasar da cin hanciu ya yi wa katutu.
'Yan Najeriya na fama da rashin ayyukan yi da kuma rashin ingantaccen ilimi da tarin kiwon lafiya mai kyau.
Ga wasu karin labaran da za ku soku karanta: