Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masana tarihi sun yi raddi kan kirkirar masarautu a Kano
Bukatar da aka ce wasu kungiyoyi sun shigar kan neman a kirkiri sabbin masarautu a Kano na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce musamman a jihar.
Masana tarihi sun fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan kudirin dokar da aka gabatar gaban majalisar dokokin jihar.
A hirarsa da BBC, Dokta Tijjani Mohammad Naniya na Jami'ar Bayero da ke Kano, ya ce "ga duk wanda ya san tarihi tambayar da zai yi ita ce mai ya kawo wannan batu."
A cewarsa ana bijiro da batutuwa a wannan sabon tsari da ake ciki na dimokradiyya da ake gani ya kamata a bai wa kowa 'yancinsa.
Sai dai a cewarsa, kamata ya yi duk abin da zai ta so ya kasance ya ta so ne daga jama'a ba wai wasu kungiyoyi ba.
Dokta Naniya, ya ce "duk da cewa ana maganar 'yanci ai ita ma majalisa jama'a ne suka zabe ta, kuma ta san nauyinta shi ne ta kare mutunci da martaba da tarihi da al'adar mutane."
"Al'ada ce ke bambanta mutumin Kano da Katsina da yadda tsarin sarautar take, hakazalika ita ke bambanta mutumin Kano da na Borno, bambancin tsarin rayuwa da masarauta da kuma yadda tsarin zamantakewar jam'a take."
Ya ce inda a ce maganar nan tasowa ta yi daga masarautu ko kuma jama'ar yankunan suna korafin cewa masarautar Kano tana yi musu wani abu da ba daidai ba, kuma suka nuna cewa dama a tarihi suna da 'yancin irin wannan sai a duba kokensu.
Masarautun dai da ake son kirkiro sun hada da Gaya da Rano da Kareye da kuma Bichi.
Sai dai Dokta Naniya ya nuna adawarsa da batun kirkiro masaurauta a Bichi inda yake cewa a tarihi da tsarin yadda sarautar Kano take Bichi ba ta da tsarin sarki.
Amma sauran kananan hukumomi kamar Rano da Gaya da Karaye fiye da shekaru 700 ko 800 da suka gabata dama suna da tarihin sarki.
Ya ce "da aka kafa su aka ci su da yaki yarjejeniyar da aka yi da su lokacin da Kano shi ne an cinye ku da yaki, amma za a baku damar ku na ku rike masarautar ku bisa tsarinku, idan sarki ya mutu daga jinsin ku za a dauko wanda zai gaje shi."
''Da Rano da Gaya da Karaye da Duste duk wannan tsarin suke da shi, amma Bichi ba ta cikin wannan tsari.''
''Tun da aka kawo wannan maganar to wani abu ne sabo, ko a baya da aka yi irin wannan tsarin a lokaci Abubakar Rimi ai abin mai dore ba.''
Har ila yau, masanin ya ce "wannan siyasa ce tsagwaranta idan kuma ana fakewa da zance 'yanci to nan gaba wasu za su fito su ce a rusa masarautar baki daya."
Kuma ya nuna fargabar cewa wannan yunkuri "na iya wargaza Kano da aka santa da kyawawan tarihi," a cewarsa.