Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wajibi ne mu yi wa Hisbah garambawul - Ganduje
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa hukumar Hisbah ta kauce hanya kuma tana bukatar garambawul.
Gwamnan, wanda ya yi magana a wajen daurin auren zawarawa da aka a yi a Kano ranar Asabar, ya bayyana cewa Hisbah tana da muhimmiyar rawar takawa wajen rage mutuwar aure a jihar amma fa sai an yi mata "garambawul sosai da sosai".
Hukumar Hisbah ce ke da alhakin tantancewa da shirya auren zawarawa, wanda gwamnatin jihar ke gudanarwa lokaci zuwa lokaci.
Zawarawa dubu 3000 ne aka aurar a wannan karon, wadanda hukumar ta ce sai da ta yi binciken lafiyarsu kafin daura masu auren.
Gwamnatin jihar ta ce ta biya kusan miliyan 30 a matsayin sadakin ma'auratan.
Da yake magana jim kadan bayan shafa fatiha, Gwamna Ganduje ya ce siyasa da rashin gaskiya sun shiga cikin hukumar Hisbah.
"Hukumar Hisbah za ta taka rawa sosai. Amma za mu yi mata garambawul don mun ga ta fara kauce hanya daga yadda aka yi ta.
"Son dukiya ya shiga wannan hukuma. Rashin gaskiya ya shiga wannan hukuma. Ci da addini da yaudara sun shiga wannan hukuma.
"Gwamnati ba za ta yarda da wannan ba. Saboda haka za mu yi mata garambawul."
Tun farko dai mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce wannan bikin aure ya zo a kan gaba, domin kwamitin da suka kafa don samar da kundin dokar zamantakewar aure ya gama ya kuma kawo rahotonsa.
Ya kuma ce dokar za ta taimaka sosai idan aka aiwatar da ita.
An yi bikin na wannan karo ba tare da shugaban hukumar ba wato Malam Ibrahim Daurawa, wanda ya kasance shugabanta har kusan shekara 10.
Dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da fadar gwamnatin jihar ne yayin da ake daf da fara kada kuri'a a babban zaben 2019.
An ga Malam Daurawa a wani faifan bidiyo tare da tawagar malamai sun kai ziyarar goyon baya ga tsohon gwamna kuma jagoran jam'iyyar PDP a jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso.
A farkon wannan shekara an yi ta rade-radin cewa gwamnatin ta kori Malam Daurawa daga mukamin nasa.
Har zuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da ke nuni da cewa an tube shi daga shugabancin Hisbah.