Sudan: Zanga-zanga ta zama gagarumin rikici

Sudanese demonstrators chant slogans during a protest demanding Sudanese President Omar Al-Bashir to step down

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dubban mutane suka shiga zanga-zangar tun a ranar Asabar

An ji karar harbe-harben bindiga a wajen shelkwatar rundunar sojojin Sudan da ke birnin Khartoum wanda a nan ne dubban 'yan kasar ke zanga-zanga na kusan kwananki uku a jere.

'Yan kasar na zanga-zangar ne inda suke bukatar Shugaban Kasar Omar al-Bashir ya sauka daga kan karagar mulkinsa.

Wadanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa sun ga mutane na gudu domin neman mafaka a lokacin da aka fara harbin.

Harbe-harben ya yi kama da kokarin gwamnatin na karshe domin tarwatsa zanga-zangar.

Daya daga cikin masu zanga-zangar Ahmed Mahmoud ya shaida wa BBC cewa jami'an tattara bayanan sirri ''sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashe,'' domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Ya bayyana cewa sojoji dauke da makamai sun killace masu zanga-zanga cikin gidajen su.

Ya ce: ''Babu amfani ga Omar al-Bashir ya ci gaba da amfani da 'yan barandansa domin hana mu zanga-zanga kan hanyoyi kuma ba za mu je ko ina ba.''

A kalla sojoji biyu ne aka bayar da rahoton mutuwarsu tun da aka fara gudanar da zanga-zangar a wajen shelkwatar rundunar sojojin.

Kokarin da jami'an tattara bayanan sirri suka yi a baya domin tarwatsa masu zanga-zangar ya jawo sojoji suka shiga domin kare masu zanga-zangar.

An ta samun kiraye-kiraye daga kasashe daban-daban inda suke kira ga gwamnati domin su guji amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

Shugaba al-Bashir ya yi kira domin a zauna a tattaunawa kan yadda za a ga an samu zaman lafiya.

Ministan harkokin cikin gida na kasar a ranar Litinin ya bayyana cewa masu zanga-zangar 17 aka kashe sai kuma mutum 15 suka jikata.

Ya kuma bayyana cewa jami'an tsaro 45 ne suka samu raunuka a kokarin da suke yi na tarwatsa masu zanga-zangar.

Ministan ya kuma ce a halin yanzu kusan mutum 2500 ne aka kama.

line

Me yasa suke zanga-zangar?

Zanga-zangar da ake yi ta ta nuna kin jini ga Shugaba Bashir an fara ta ne watanni da dama.

Shuagaba Bashir ya fara mulkin kasar tun a 1989.

Asalin zanga-zangar ta fara ne a lokacin da aka samu hauhawan kayayyaki a kasuwa inda daga baya kuma zanga-zangar ta sauya akala inda suke bukatar da shugaban ya yi murabus.

Zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images

Wane martani aka mayar?

Wani bidiyo na ban mamaki da ya fito a ranar Litinin ya nuna sojoji na harbi ta ko ina inda fararen hula na kokarin neman mafaka.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa sojojin na mayar da harbin ne ga jami'an hukumar tattara bayanan sirri.

President Omar al-Bashir sitting on a green chair dressed in white at the National Dialogue Committee at his palace in Khartoum on April 5

Asalin hoton, Reuters

Wadanda suka shaida lamarin sun yi zargin cewa sojojin sun yi harbin gargadi a lokacin da suke kokarin korar jami'an.

Ministan watsa labarai na kasar Hassan Ismail ya musunta rahoton rabuwar kan da aka samu tsakanin jami'an.

Ya bayyana cewa ''hukumomin tsaron kansu a hade yake kuma suna aiki tare.''

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi kira ga dukkanin bangarorin da su yi hakuri da juna kuma su guji tashin hankali.

Map of Khartoum showing where protesters are gathered

Gwamnatin kasar ta bayyana cewa mutane 38 ne suka mutu tun bayan da aka fara zanga-zangar a watan Disambar bara amma kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce yawansu ya dara haka.

Me yasa ake takaddama da shugaban kasar?

Ana sukar mulkin Mista Bashir da take hakkin bil adama.

Ana ganin cewa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na da yiwuwar bayar da takardar sammaci a gareshi sakamakon zarge-zargen da ake yi masa na kisan kiyashi da kuma laifuffuka da suka shafi yaki da kuma laifin take hakkin bil adama.

Amurka ta saka wa kasar takunkumi shekaru 20 da suka gabata inda Amurkar ke zargin Khartoum da daukar nauyin kungiyoyin 'yan ta'adda.

A bara, darajar kudin Sudan ya fadi warwas wanda hakan ya yi sanadiyar samun tashin gwauron zabin kayayyaki.

A watan Fabrairu, an yi zaton shugaban zai yi murabus, amma sai aka ji kwatsam shugaban ya sa dokar ko ta kwana.

line