Sudan ta dakatar da aikin 'yan jarida

Asalin hoton, Reuters
Hukumomi a Sudan sun janye izinin da suka bai wa wasu 'yan jaridar kasashen waje biyu.
Kasar ta fada tsundum cikin rikici tun bayan da gwamnatin kasar ta kara farashin man fetur da na biredi a cikin shekarar da ta gabata.
Wannan na nufin 'yan jaridun ba za su iya aika wa da rahotannin abubuwan da ke faruwa a cikin kasar ba kenan, a daidai lokacin da zanga-zangar kin jinin gwamnati ta shiga mako na shida.
Wadannan 'yan jaridar na yi wa kafofin watsa labarai na Al Arabiyya ta Saudiyya da Anadolu, kamfanin dillancin labarai na Turkiyya.
Hukumomin Sudan sun ce za su sabunta rajistar aiki ta 'yan jaridar ne, amma ba su bayar da wani karin bayani ba.
Majalisar harkokin yada labarai ta Sudan, wadda ke da alhakin ba kafofin watsa labarai na kasashen waje izinin aiki a kasar ta ce dakatarar za ta ci gaba har sai abin da ta kira "sai an kammala duba cancantar su ta yin aiki a Sudan".
Rikici ya barke a kasar a watan jiya saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar, amma lamarin ya sauya ga yunkurin sauke shugaba Omar al-Bashir wanda ya shafe shekara 30 a bisa karagar mulkin kasar.
Jami'an gwamnati sun ce akalla mutum 26 ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar wannan rikicin, amma kungiyoyi masu rajin kare hakkin dan Adam a kasar sun ce alkaluman wadanda aka kashe sun zarce mutum 40.









