Me ya sa 'yan Sudan ke boye kudi a karkashin katifa?

Asalin hoton, Reuters
A cikin takardun da mu ke samu daga 'yan jarida na Afirika, Zeinam Mohammed Salih ta yi dubi a kan dalilan zanga-zagar da ake yi na nuna rashin jin dadin mulkin Omar al-Bashir da ya shafe shekaru 30 yana shugabanci a Sudan.
Mutane da dama a Sudan sun fi so su boye kudaden su karkashin katifa maimakon su kai banki ajiya.
Idan mutane suka kai kudin su banki, suna shan wahala kafin su same su saboda wahalar da suke sha wajen cire kudin daga na'urar ATM.
Duk inda na'urar ATM ta ke a Khartoum kuma akwai kudi a ciki, to akwai yawan layi a ciki.

Haka ma, ana samun layin biredi.
Bayan na dawo daga aiki da dare, na kan jira fiye da sa'a daya a gidan biredi sai wani lokacin a ce biredin ya kare.
Kayan abinci daban-daban suna kara tsada a kullum a babban birnin kasar.
Abinci kamar wake ana samun shi a kowane lungu a wannan gari, amma shagon da ke makwabtaka da ni sun daina sayarwa saboda mutane da dama ba su iya saya saboda karin farashi.
Bayan na dawo daga tafiyar da na yi ta wata shida, na ga mutane da dama sun rame.
Cire tallafi
Wannan matsalar ta kunno kai ne a dai-dai lokacin da gwamnatin kasar ta yi kokarin kawo wasu tsare-tsare domin kokarin kaucewa durkushewar tattalin arziki da kuma rage darajar kudin kasar.
A watan Disemba ana samun dala 1 a kan fam 76 na kudin Sudan a kasuwar bayan fage, inda wata shida da suka wuce ana samun dala daya a kan fam 40 na Sudan.

Asalin hoton, AFP
Ana kara samun hauhawan farashi da kusan kashi 68 cikin 100 a Nuwamba inda a 2016 aka samu da kashi 25 cikin 100.
A cikin matakan da aka dauka na farfado da tattalin arzkin kasar, gwamnatin ta rage tallafi a kan biredi da man fetur wanda hakan ya kara jawo hauhawan farashin kayayyaki.
Karin kudin biredi a watan da ya gabata ne ya rura wutar da ta jawo zanga-zangar da har yanzu ake yi.
Sun fara zanga-zangar ne a gabashin garin Atbara 19 ga watan Disemba inda aka kona shelkwatar jam'iyyar NCP.
Juyin juya hali na kasashen Larabawa
Wadannan abubuwa sun janyo zanga-zanga inda ake kira ga Omar al-Bashir ya sauka daga kan karagar mulki bayan ya shafe fiye da shekaru 30 a kai.
Masu zanga-zangar wadanda suke ihun cewa ''muna so mu ga karshen wannan mulkin."
Wannan zanga-zangar ita ce wacce ta fi kamari tun bayan hawan mulkin Bashir a 1989.
Abubuwa dai suna kara kazanta.
Hukumomi sun ce mutane 19 sun mutu a kokarin da aka yi na kwantar da tarzomar amma kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta bayyana cewa tana da rahotanni a kan cewa mutane 37 ne aka kashe sakamakon zanga-zangar.
An kama masu zanga-zangar da dama kuma an ci mutunci da kama wasu 'yan jarida a kokarin da suke yi na tattara rahotanni a kan zanga-zangar.
Karin bayanai a kan Sudan
Wannnan dai ya karo matsin lamba ga shugaban mai shekara 75 wadanda mutane ke korafin cewa sun ga ya fara rudewa da rikicewa a lokacin da yake ganawa da shugabannin 'yan sanda a makon da ya gabata.
Shugaban dai ya bukaci jami'an da kada su yi amfani da karfi a kan masu zanga-zangar amma ana ganin kamar ya yi amai ya lashe sakamakon wasu kalamai da ya yi a baya.

Asalin hoton, Getty Images
Masu sharhi dai sun fassara kalaman shugaban a kan wata dama da aka bayar na daukar tsattsauran matakai a kan masu zanga-zangar.
Washegari ne dai dubban mutane suka fito a cikin Khartoum domin zanga-zanga inda aka harbi mutum hudu.
A bangaren gwamnatin, ta zargi wasu mutane daga yammacin Darfur a matsayin masu hannu wajen zanga-zangar da lalata kayan gwamnati.
An dai kama gungun wasu dalibai 'yan Dafur wadanda ba Larabawa ba ne inda ake zargin cewa hukumar leken asiri ta Isra'ila ce ta horar da su.
Abokansu dai sun musanta hakan inda suka zargi gwamnatin kasar da dora laifi a kan daliban.

Asalin hoton, AFP
Shugaba Bashir ya yi alkawarin karin albashi ga ma'aikata domin rage matsaloli, amma ana ganin hakan ba zai kwantar da kurar da ta taso ba.
A ranar Laraba, ya gargadi Syria a wurin wani taro a Khartoum inda ya ce rashin zaman lafiya zai iya sa 'yan kasar su zama 'yan ci-rani.
Kasar dai ta dade tana fama da matsalar tattalin arziki tun bayan ficewar Sudan ta Kudu a 2011 inda Sudan ta Kudu ke da mafi yawan arzikin man fetur.











