Miji ya yi wa matarsa kwalkwal saboda ta ki yin rawa

Asma Aziz
Bayanan hoto, Asma Aziz na neman a bi mata hakkinta a bidiyon da ta wallafa

Wata mata 'yar kasar Pakistan na tuhumar mijinta da yi mata duka da kuma aske mata gashin kanta don ta ki amincewa ta yi rawa a gaban abokan mijin nata, lamarin da ya ja hankali game da kare hakkin mata a kasar.

Asma Aziz 'yar yankin Lahore ta janyo hankalin mutane lokacin da ta yada bidiyon mai daga hankali a shafukan sada zumunta da ya nuna anyi mata kwal kwabo .

Mijinta mai suna Mian Faisal da mai aikinsa na hannun 'yan sanda, duk kuwa da cewa ya musanta faruwar lamarin.

Kazalika, ana ta samun kiraye-kiraye game da daukar mataki don kare mata daga kalubalen da suke fuskanta a gidan aure.

A wani sakon twitter, hukumar kare hakkin bil'adama ta kasar ta ce, " ya zama dole a samu sauyi a lamarin".

A cikin bidiyon da ta wallafa ranar 26 ga watan Maris, Aziz ta fuskanci wannan hukunci ne bayan da ta ki amincewa ta yi rawa a gaban abokan mijinta a cikin gidansu da ke Lahore.

Ta ce, "Ya yi min tsirara a gaban hadimansa, wadanda suka rike ni shi kuma ya aske min gashi ya kuma kone shi''

Ta kara da cewa, ta kai korafi wajen 'yan sanda amma sun ki mayar da hankali kan lamarin, suka kuma musanta hakan, inda suka ce Aziz na barin ofishin 'yan sandan suka isa gidanta, amma suka tarar da gidan a garkame kuma aka hana su shiga ko da harabar gidan.

A yanzu haka dai Mista Faisal da mai hadiminsa Rashid Ali na hannun 'yan sanda.

'Yan sandan sun dauki mataki ne kawai bayan da bidiyon ya isa ga mataimakin ministan harkokin cikin gida na kasar, Sheheryar Afridi, wanda ya umarci jami'an su saurari korafin.

Mista Faisal ya shaida wa 'yan sanda cewa tun a makon da ya gabata ne matar tasa ta fara aske gashin kanta sakamakon mayen da ta shiga bayan da ta sha kwaya ta bugu, a saboda haka ne shi kuma ya taimaka ya karasa mata aikin da ta faro bayan da shi ma ya sha tasa kwayar.

A binciken da aka gudanar yanzu an samu rahoton raunuka da dama a jikin Aziz, wanda ya hada da hannunta, da kuncinta da kuma gefen idonta na hagu.

Masu fafutika sun ce ba a bayyana hakikanin alkaluman yawan matsalolin da ake da su a hukumance ba, yawancinsu ana barin su ne ba a fada.

Ko a ranar mata da duniya da aka yi a watan jiya an samu korafe-korafe daga wasu kungiyoyi. Wasu daga cikinsu sun ce sun samu labarin mace-mace da kuma yi wa mata fyade a shafukan sada zumunta.