An yi wa Buhari ca kan nuna alhinin wanda aka kashe a Lagos

Asalin hoton, Getty Images
'Yan Najeriya da dama sun yi caa da suka kan Shugaba Muhammadu Buhari, kan alhinin da ya nuna na mutuwar wani mutum a Legas, suna masu zargin shugaban da cewa ya yi buris da halin da al'ummar jihar Zamfara ke ciki na kashe su da ake yi a kusan kowace rana.
Shugaban Buhari dai ya jajanta wa iyalai da abokan arzikin Mista Kolade Yusuf da ake zargin 'yan sanda ne suka kashe a Legas a ranar Lahadi.
A wani sako da fadar shugaban kasar ta wallafa a Twitter ranar Litinin, ta bayyana cewa wadanda ake zargi da kisan an kama su kuma suna fuskantar tuhuma kan lamarin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Sai dai wannan sakon jajen na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotanni na kisan gilla da 'yan fashi ke yi a Zamfara da kuma wasu sassa a Najeriya, tare kuma da sace mutane don neman kudin fansa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Bayan da fadar shugaban kasa ta wallafa wannan sako a shafinta naTwitter, jama'a da dama sun ta kawo suka kan zargin bambancin da shugaban ke nunawa.

Asalin hoton, Police
Akasarinsu sun bayyana cewa an yi kashe-kashe a Zamfara da wasu wurare amma shugaban bai jajanta ba ko da a shafukan sada zumunta.
Sai dai BBC ta yi kokarin jin ta bakin fadar shugaban kasar kan korafin na jama'a amma abin ya ci tura.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Karshen labarin da aka sa a X, 4
A wannan makon ne aka samu rahotanni da ke cewa an kashe a kalla mutane 42 a Zamfara, sai dai hukumomi sun ce mutane 28 ne aka kashe a bincikensu.
Sannan kuma ana sake samun rahotannin sace mutane a sassa daban-daban na arewa maso yammacin kasar.
Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya bayyana tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da kuma tattalin arziki a matsayin abubuwan da ya sa a gaba domin kawo ci gaba a kasar.
Har yanzu wasu na nuna gazawar gwamnatin ta fannoni daban-daban a wadannan bangarori.