Buhari bai yiwa Arewacin Najeriya komai ba – Bafarawa
Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren hirar da Attahiru Bafarawa ya yi da Mustapha Musa Kaita
Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa ya caccaki Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dangane da salon mulkinsa musamman rawar da yake takawa ga arewacin kasar.
A hirarsa da BBC, Bafarawa ya bayyana rashin tsaro a matsayin babbar matsalar da kasar ke fuskanta, inda ya bayyana matsalar garkuwa da mutane don karbar kudin fansa a matsayin abin da ya ki ci, ya ki cinyewa.
Ya bayyana cewa bai ga wani ci gaba da aka samu ba a kasar, inda ya ce gara gwamnatin baya da ta yanzu.
Bafarawa ya bayyana cewa "bai taba jin shugaban kasar ya zauna da gwamnonin arewa ba, domin tattauna matsaloli da kuma mafitar arewa."
Har ila yau, tsohon gwamnan ya ce ana nuna bangaranci wajen gudanar da ayyukan ci gaba a kasar.
Ya yi kira ga shugaban kasar da ''ya bude kunnunwansa domin sauraren shawarwari da za su iya kawo ci gaba a kasar.
Kalaman na Bafarawa na zuwa ne bayan lashe zabe da Shugaban Najeriyar ya yi karo na biyu.
Tun a baya dai, Shugaban Najeriyar ya bayyana tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da kuma tattalin arziki a matsayin abubuwan da ya sa a gaba domin kawo ci gaba a kasar.












