'Ciwon da ya saukar min da radadi a al'aurata'

25-year-old Georgia
Bayanan hoto, Georgia na fuskantar ciwo mai naci a al'aurarta.

"Babu abin da ya kai shi ciwo a duniya, ji za ka yi kamar ka bayar da duk abin da ka mallaka don ya daina."

Haka Georgia ta bayyana yadda ta rika fama da ciwon da ake kira vulvodynia.

'Yar shekara 25 din mai zane-zane 'yar Manchester a Birtaniya ta ce zane ya taimaka mata jure radadin ciwon.

Mene ne cutar vulvodynia?

Hukumar lafiya ta Birtaniya (NHS) ta bayyana vulvodynia a matsayin wani irin ciwo da ba a san abun da ke jawo shi ba kuma mai naci a fatar da ke wajen al'aura.

Haka na nufin cewa Georgia na fuskantar matsanancin ciwo a wajen al'aurarta.

Georgia looking out a window
Bayanan hoto, Sai da aka kwashe tsawon shekara biyu kafin Georgia ta san abin da ke damunta.

Mata manya da yara na kamuwa da matsanancin ciwon kuma mata masu isasshiyar lafiya ma kan kamu da shi.

Sanya kunzugu lokacin al'ada ko yin jima'i ko dadewa a zaune na kawo wannan radadin ciwo, in ji hukumar lafiyar Birtaniya.

Alamun ciwon

Presentational grey line
  • Radadi ko suka ko zinga
  • Ya fi tashi idan aka taba fatar wajen kamar lokacin jima'i ko a lokacin sa kunzugun al'ada
  • Ba ya daina radadi kuma zafin kan karu idan ana zaune
  • Iyakar fatar wajen al'aura ake jin ciwon
  • Wani lokaci zafin ciwon kan gangara duwawu da tsakanin cinyoyi

Majiya: NHS

Presentational grey line

A lokacin da take bayyana alamun da ta rika ji, Georgia ta ce: "Na fara jin wani irin zafi. Idan na zauna sai in ji wani irin radadi."

Georgia ta ce ko ta je wajen likitoci su kan nuna mata cewa ba wani abu ba ne.

"Na je wajen likitoci sai suka ce 'Ai ba wani abu ba ne, kawai ciwon kaikaiyin gaba ne', ko kuma su ce 'Ai irin cututtukan nan ne da ake dauka a wajen saduwa'"

"Da alamu ba wadannan abubuwan ba ne saboda da mutum daya nake tarawa kuma ba ciwon kaikayin gaba ba ne don na san yadda yake," a cewarta.

Georgia's hands
Bayanan hoto, Cikin alamun da Georgia ke ji har da wani irin radadi kamar ta kone

Georgia ta ce wata rana hakurinta ya kare: "Na gama wanka kuma gaba daya zafin ciwo ya dame ni. Na zauna na kankame kafafuwana ina kuka kuma ina fatan in daina jin ciwon nan. A lokacin ji nake kamar babu abin da ba zan yi ba don in daina jin azabar ciwon."

Daga baya aka gano cewa tana da cutar vulvodynia.

Tana gane haka, sai ta fara duba abubuwan da ke tayar da ciwon kuma ta yi sauye-sauye a rayuwarta. Ta sauya irin dan kamfai da take sawa kuma ta rage shan barasa.

"Idan na sha giya, lallai washegari zan tashi da matsanancin ciwo," ta bayyana.

Georgia looking at her picture
Bayanan hoto, Zane na taimaka wa Georgia wajen dauriya

Bincike ya gano cewar cutar vulvodynia ba ta da magani, amma ana iya shan magani don a samu sauki.

Wani bincike da aka buga a mujallar lafiyar mata ta kasa da kasa a shekarar 2016, ya ce kashi 16 cikin 100 na mata a Amurka na fama da ciwon.

Zane ya taimaka wajen jure ciwo

Georgia ta ce zane ya taimaka mata wajen jure ciwon da take fama da shi.

"Akwai lokutan da na kan ji komai ya gundure ni, sai in dauki abin rubutu da takarda in fara zane sai in ji sauki a raina."

Duk da cewa Georgia ta bayyana yadda ciwon ya wahalar da ita, tana da sakon da take so ta aika wa duk wata mace da ke fama da irin cutarta.

"Ina so mata su sani cewa ina jin tsoron magana kan ciwona, amma ba abin kunya ba ne, kawai dai da wahala amma haka nan za a daure a ci gaba da rayuwa da shi."

Presentational grey line