Dangantakar Sarauniya Elizabeth da Diana

Asalin hoton, PA
A wajen Sarauniya dai, karshen lamarin shi ne "yarinyar da ba za ta taba samun shiga (a wajenta) ba." Ita kuwa Diana a wajenta, ta yi ikirarin nuna "kauna" ga surukarta, kuma za ta iya yin komai dominta.
Sai dai ta yiwu ba haka lamarin yake ba a wajen Sarauniya, bisa la'akari da irin tasirin Gimbiyar Wales ga sarauta, a daukacin rayuwa da mutuwa.
Auren da ta yi a gidan sarauta wani babban yunkuri ne a wajen kowane mutumin da ke hange daga gefe, kai hatta ma wadanda suka shaku da rayuwar Diana.
Matashiya Diana, haifaffiyar madaukakiyar zuri'a ce, wadda ta shafe shakarun rayuwarta na farko a farfajiyar Park House, wani gini dan taki ne daura da gidan Sarauniya na Norfolk da ke Sandringham.

Asalin hoton, PA
Sai dai ta bayyana karara ba tare da bata lokaci ba, cewa Diana mai shekara 20 ba ta shirya yin rayuwa irin ta wadanda suka dan manyanta a harkar fada.
Ba ta samu agajin mutumin da zai kasance mijinta a cikin rayuwa ba.
Ya kasance mai ra'ayin rikau, kuma dabi'arsa ta yi matukar saba wa na amaryarsa mai karsashi da far-far da jin kunya, sannan ga shi ya darsu da kaunar tsohuwar masoyiyarsa Camilla Parker-Bowles.
Rashin karsashinsa kan "dukkan abin da ya danganci soyayya," a amsar da ya bai wa mai neman labari da ya bijiro masa da tambaya kan yadda yake ji lokacin baikonsa, don share fagen kulla alakar (da abokiyar zaman) nan gaba a cikin rayuwa.
Sarauniya dai ta yi wa kanta sharadin ba kasafai takan tsoma baki a harkar auren 'ya'yanta ba.
Yanayi
Wasu masu sharhi sun yi nuna cewa kamata ya yi a ce ta shiga harkokin sarauta ka'in da na'in duk da kasancewarta sabon shiga da an tallafa mata.
Diana ta yi fama da kadaici, tare da rashin sanin inda ta dosa - kuma ba ta da tabbacin abin da ake bukata daga gareta, don haka ta kasance cikin bacin rai, saboda rashin yaba wa nagartar kyakkyawan aikinta.
Sarauniya, tamfar Yarima Charles, ta dauki babatu (cika da batsewar) Gimbiya abin takaici, kuma mawuyacin abin da za a iya shawo kansa.. Lamarin ya sha gabanta gogewarta a rayuwa, bisa la'akari da yadda ta taso, inda ba a baje abin da sosuwar zuciya ko damuwar mutum a bainar jama'a.

Kai tsaye dai ba su san yadda za su tarairayi irin yanayinta da irin yadda ta darsu da son a ba ta cikakkiyar kulawa - kamar yadda takan bararraje a matattakalar bene lokacin da take dauke da cikin William.
Ba haka ake yin irin wannan a zuri'ar gidan sarauta ba.
Kuma ba su shirya wa yadda Diana ta rika juya akalar 'yan jarida suka yi ta haifar da ce-ce-ku-cen jan ra'ayin jama'a game da ita ba.
Sarauniya ta yi takaicin tarwatsewar auren da aka yi wa alwashin samun dimbin alfanu.
Daga nesa ta yi ta nazarin al'amuran da ke faruwa, inda ta yi kokarin kamewa - bisa tabbacin da take da shi cewa kasa kai ga gacin danta da auren magajinta na iya yin mummunar illa ga sarauta.
Muhimmin abin lura
Lokacin da dangantakar Charles da Diana ta yi tsami, sai ta yi watsi da dabi'arta ta rashin yin katsalandan (tsoma baki a harkar auren 'ya'yanta), sai ta kira su don tatttaunawa, inda ta shawarce su kan su yi kokari na karshe wajen shawo kan matsalar aurensu..
Lamarin dai ya ki yiwuwa, har sai da ta kai ga ba da dadewa ba, Diana ta yanke matsaya wajen bayyana wa al'umma halin da take ciki a shirin hangen nesa na BBC (Panorama), sai Sarauniya ta sake shiga cikin lamarin, inda ta rubuta wa kowanensu wasika, tare da nunin cewa rabuwar aurensu a halin da ake ciki ita ce kawai mafita.
Saboda jikokinta, Sarauniya ta yi matukar iya kokarinta wajen kyautata dangnatakarta da Diana, amma bayan da auren ya rabu, sai ta kara nesanta kanta da ita.

Asalin hoton, Reuters
Bayan mutuwar Diana, an zargi Sarauniya da rashin fahimtar yadda mutanen kasar ke ji lokacin da ta tare a Baltimore don kwantar da hankalin jikokinta da ke cike da alhinin rashi.
Karshe dai aka karke da kambama labarin a jaridu da dama, al'amarin da ya tursasata ta komo Landan.
Lokacin da aka yi nisa da jana'izar Diana sai kwatsam ta yi wani jawabi kai tsaye ta talabijin, inda ta yi bayani kai tsaye game da surukarta.
An ji cewa tamkar Sarauniya ta jefa harkokin sarauta cikin musifa.
Taro ne mai matukar kayatarwa da ke nuna tausasawa da gudunmuwa ga al'umma.
Lokacin da aka wuce da makarar gawar Diana ta gaban Fadar Buckingham, sai Sarauniya ta yi mata karramawar ban kwana..
Ta russuna don karrama wannan matashiya da ta samu kauna da girmama a wajen mutane da dama, amma dai sanadiyyar surukarta, wadda ta kasance mai ban mammaki tsawon rayuwarta.
©Hakkin mallakar hotunan abun kiyayewa ne











