'Yan Najeriya suna zargin Buhari a kan raguwar kudin Dangote

Dangote ya fi samun kudi daga siminti

Asalin hoton, ERIC PIERMONT

Bayanan hoto, Dangote ya fi samun kudi daga siminti
Lokacin karatu: Minti 1

Hamshakin dan kasuwar nan a Najeriya Aliko Dangote har yanzu shi ne wanda ya fi kowa kudi a Afirika amma yawan kudin nasa sun ragu.

Mujallar Forbes ta wannan shekarar ta wallafa cewa har yanzu sunan Dangote ne a farko a jerin masu kudin Afirika da dala biliyan 10.3.

Wannan na nuna cewa kudin nasa sun ragu da kusan dala biliyan 2.

Mujallar Forbes din ta nuna cewa matsalar kasuwa ce da kamfanin siminti na Dangote ya fuskanta ya jawo raguwar kudin.

Mike Adenuga, shugaban kamfanin sadarwa na Globacom shi ne yazo na biyu a jerin sunayen masu kudin da kusan dala biliyan 9.2.

A bara dai jimlar kudin Mike din dala biliyan 5.3 ne.

Da dama masu sharhi a shafukan sada zumunta musamman Twitter suna dora laifin raguwar kudin Aliko Dangote a kan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Monitoring Spirit ya ce "Kudin Dangote a 2014 dala biliyan 25 sun ragu zuwa biliyan 10 a 2018 a cewar mujallar Forbes....Sai Baba."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Makinde David ya ce "Idan mun ga laifin Buhari a kan raguwar kudin Dangote, me yasa hakan bai faru da Adenuga ba? Hakan na bani mamaki."