Abin da ya sa ba zan rage farashin siminti ba – Dangote

Bayanan bidiyo, Aliko Dangote

Shahararren dan kasuwar nan na Najeriya Alhaji Aliko Dangote ya bayyana dalilan da suka sa ba zai iya rage farashin siminti ba, kamar yadda gwanatin kasar ta nema.

A kwanakin baya ne mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya bukaci Dangote da mai kamfanin BUA Abdussamad Isyaku Rabiu su rage farashin siminti.

Dangoten ya kuma yi karin haske kan inda aka kwana dangane da aiki matatar mai da yake ginawa.

A tattaunawar da suka yi da wakilin BBC Nasidi Adamu Yahaya, attajirin na Afirka ya bayyana cewa an kusa kammala aikin matatar man.