An 'murkushe' masu juyin mulki a Gabon

Gabon's president Ali Bongo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaban Gabon ya yi wata biyu a waje

Wani mai magana da yawun gwamnatin Gabon ya ce al'amura sun koma daidai bayan yunkurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi.

Guy-Bertrand Mapangou ya shaida wa BBC cewa an kama hudu daga ciki 'yan tawayen, yayin da na biyar din ya tsere.

Wasu kananan hafsoshin ne suka kwace iko "don maido da dimokradiyya" a kasar mai arzikin man fetur, kasar da iyalan shugaba mai ci da suka mulki kasar tsawon shekara 50.

An ga tankoki da motoci dauke da makamai a birnin Libreville.

Sojoji sun karbe iko da gidan rediyon kasar da misalin karfe 04:30 (03:30 agogon GMT) inda suka yi wata gajeruwar sanarwa.

Shugaban kasar Ali Bongo ya gaji mahaifinsa Omar Bongo a shekarar 2009.

Sai dai ya lashe zaben shekarar 2016 a wani zabe da ake zargin an tafka magudi.

Wakilin BBC Firmain Eric Mbadinga ya ce yunkurin juyin mulkin ya ba mutane mamaki.

Ana ganin sojoji suna biyayya ga iyalan Bongo saboda galibinsu daga yankin da iyalan Shugaba Bongo suka fito ne.

Rahotanni na cewa Shugaba Bongo ya sami matsalar shanyewar wani bangare na jikinsa ne a Oktoba kuma yana jinya a kasar Maroko.

A sakonsa na sabuwar shekara shugaban ya yi wa al'ummar kasar jawabi ta kafofin watsa labarai domin gamsar da su inda ya ce yana samun sauki.

Sojojin sun ce jawabin nasa bai gamsar da su ba, inda suka ce "wannan wani kokari ne na kankamewa ga mulki".