Shugaban kasar Gabon 'yana fama da matsananciyar rashin lafiya '

Asalin hoton, Reuters
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo yana fama da matsananciyar rashin lafiya ko da yake yana samun sauki, in ji mai magana da yawunsa, abin da ya kawo karshen gum da bakin da aka kwashe makonni ana yi kan batun.
An yi ta yada jita-jita kan rashin lafiyar Shugaba Bongo, mai shekara 59, inda wasu ke cewa barin jikinsa ya shanye.
Yan kwance a wani asibitin Saudiyya, inda rahotannin da aka bayar a watan jiya suka ce fama da cutar matukar gajiya.
Mai magana da yawunsa Ike Ngouoni ya ce Mr Bongo yana "dukkan gabbansa suna samun sauki".
Bai ce komai a kan rahoton shanyewar barin jikin shugaban kasar ba, amma Shugaba Bongo ya yi fama da "zubar jini wanda ke bukatar kula da lafiyarsa", in ji Mr Ngouoni.
A shekarar 2009 ne Ali Bongo ya gaji mahaifinsa Omar Bongo, wanda ya mulki kasar fiye da shekara 40, a matsayin shugaban Gabon.
Ya sake zama shugaban kasa da kyar a 2016 a zaben da aka gudanar mai cike da rikici da zargin magudin zabe.
A farkon watan nan, lokacin da Shugaba Bongo ya je Riyadh, babban birnin Saudiyya, shi kuma jarogaran jam'iyyar hamayya ta Gabon Jean Ping ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben kasar.
Ranar Juma'a aka dakatar da wata jarifdar Gabon tsawon wata uku saboda da ikirarin da ta yi cewa "babu wanda yake jan ragamar mulkin" kasardon haka ya kamata firai minista ya nada shugaban rikon kwarya.











