'Ya kamata Najeriya ta koma tsarin Firaiminista'

Wasu 'yan majalisar dokokin Najeriya sun fara wani yunkurin na ganin an sauya kundin tsarin mulkin kasar, ta yadda za a bar tsarin shugaba mai cikakken iko zuwa tsarin faraiminista.

'Yan majalisar sun ce sun dauki wannan mataki ne saboda yawan sabanin da ake samu tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa, da kuma makudan kudin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.

Daya daga cikin 'yan majalisar da suka gabatar da kudirin, Honourable Muhammad Musa Soba, ya shaidawa BBC cewa kudirin da tuni aka yi wa karatun farko 'yan majalisar 71 ne suka sanya hannu kafin gabatar da shi.

Ya ce daga cikin abubuwa da suka duba kafin bijiro da wannan kudiri akwai yawan kudin da ake kashewa a tsarin da kasar ke kai a yanzu da kuma adadin ma'aikata da ke aiki a fadar shugaban kasar da su kansu yawan 'yan majalisu da suka haura 460.

Dan majalisar ya ce, tun shekara ta 1999 ake ganin yadda shugaba mai cikakken iko a Najeriya ke ruwa da tsaki wajen sauya shugaban majalisa, kuma a cewarsa hakan na haifar da tarnaki ga ayyukansu la'akari da yada ake sa-in-sa tsakanin majalisar zartarwa da ta dokoki.

Hon. Mohammad ya kuma ce ba su damu da yadda tsarin zai iya shafarsu ta fanin rage yawan 'yan majalisu da kuma irin makudan kudaden da ake kashe musu ba, domin burinsu shi ne ceto kasar.

Dan majalisar ya kuma kara da cewa bijiro da wannan kudiri a yanzu ba shi da alaka da yanayi na siyasa ko karatowar zabe domin a ganinsu lokaci ne ya yi na soma irin wannan tunani a kasar.