Dama can an shirya kashe Khashoggi - Erdogan

Asalin hoton, Reuters
Shugaban kasar Turkiyya ya shaida wa 'yan majalisar dokoki na jam'iyyarsa cewa an shirya kashe dan jaridar nan mai suna Jamal Khashoggi kwanaki kadan kafin mutuwar tasa.
Ya ce Turkiyya na da kwakkwarar shaidar da ke nuna cewa an kashe Khashoggi ne a wani lamari da aka shirya na yi masa kisan gilla a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Santanbul, ranar 2 ga watan Oktoba.
Ya kuma yi kira da a yi wa wadanda ake zargi shari'a a Santanbul.
Ya bukaci Saudiyya ta samar da amsoshi kan inda gawar Khashoggi take da kuma wanda ya bayar da umarnin aikata kisan.
Masarautar Saudiyya dai ta bayar da bayanai daban-daban masu rikitarwa a kan abun da ya samu dan jaridar, wanda yake kuma rubuta makaloli a jaridar Washington Post a wasu lokutan.
Bayan an shafe makkonni tana cewa yana nan da ransa bai mutu ba, a yanzu kuma hukumomi sun ce an kashe shi ne yayin wata hatsaniya a ofishin jakadancin nata.
Jawabin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya gabatar a ranar Talata ya zo daidai da fara taron zuba jari na Saudiyya, wanda batun kisan Khashoggi zai mamaye, inda gomman gwamnatoci da manyan 'yan kasuwa ke janyewa daga taron.
Me shugaban kasar Turikyya ya ce?
Shugaba Erdogan ya tabbatar da cewa an kama mutum 18 a Saudiyya kan wannan lamari. Sai dai bai yi karin bayani kan hujjojin da ya samu game da kisan ba.
Bai yi magana a kan wata murya da aka nada ko wani bidiyo ba da aka ambata a rahotanni a kwanakin da suka biyo bayan batan dan jaridar.
Shugaba Erdogan ya ce tawaga uku ta 'yan asalin Saudiyya sun isa Santanbul a jirage daban-daban a kwanaki kadan da suka rage a aikata wa Mista Khashoggi kisan gillar.
Mista Erdogan ya shaida wa 'yan majalisar jam'iyyarsa ta AK cewa: "Abun da nake so shi ne a yi wa wadannan mutum 18 hukunci a Santanbul, da ma duk wadanda suke da hannu a kisan gillar."











