Shigar IS rikicin Boko Haram ta kara dagula lamura ne?

    • Marubuci, Ishaq Khalid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Ana dai dora laifin karuwar zaman dar-dar din a wannan lokaci a kan kungiyar nan da ke ikirarin kishin Islama ta IS, da kuma tankiya da ake fuskanta gabanin manyan zabukan da za a yi a Najeriya.

Hauwa Liman da Saifura Ahmed Khorsa dukkaninsu suna aiki ne da kungiyar Red Cross ta kasa da kasa wato ICRC lokacin da aka sace su tare da wata ma'aikaciyar agajin a garin Rann da ke jihar Borno a cikin watan Maris.

Mayaka daga wani bangare na kungiyar Boko Haram mai biyayya ga kungiyar IS ne suka sace matan.

Wannan bangare na Boko Haram na kiran kansa Kungiyar IS a Yankin Yammacin Afirka ko kuma ISWAP a takaice.

A watan Satumba aka kashe Saifura mai shekara 25, sannan bayan wata guda kuma aka kashe abokiyar aikinta, Hauwa, mai shekara 24.

'Yan jarida na cikin gida, wadanda suka kalli hotunan bidiyo biyu da mayakan masu ikirarin jihadi suka fitar bayan kashe-kashen na gilla, sun ce matan na sanye ne da hijabai kuma an tursasa masu durkusawa, hannuwansu kuma na daure.

Daga nan sai aka bindige su.

Ana ci gaba da garkuwa da daliba

Tun farko kafin su kashe ma'aikaciyar Red Cross Hauwa, mayakan sun ba da wa'adin cewa idan ba a biya masu bukatunsu ba za su kashe ta, kuma suka aikata hakan.

To amma babu tabbaci kan irin bukatun da suka gabatar. Ko ma mene ne dai, ga alama ba a biya masu bukatun ba.

Kungiyar ISWAP wacce aka yi imanin tana samun umarni daga hedikwatar kungiyar IS ne da ke yankin Gabas ta Tsakiya, ta kara fitowa fili ne a wannan shekarar.

An yi imanin ita ce ta sace 'yan mata 'yan makaranta 110 a garin Dapchi da ke jihar Yobe a watan Fabrairu.

Bayan wata guda, an saki galibin 'yan matan, in ban da wata mai shekara 15 wadda aka ce ta ki karbar addinin Musulunci, don haka mayakan suka ci gaba da garkuwa da ita.

Ga alama dai ISWAP ita ce mafi karfi cikin bangarorin kungiyar Boko Haram tun bayan da aka samu rarrabuwar kawuna a kungiyar ta Boko Haram bisa rikicin shugabanci a watan Agustan 2016.

Kungiyar Boko Haram dai ta kaddamar da ayyukanta na tayar da kayar baya ne kimanin shekeara tara da suka gabata, inda ta kwace iko da yankuna masu girman gaske a arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban Boko Haram din ya kara yin kaurin suna a duniya, bayan sace 'yan mata 'yan makarantar Chibok fiye da 200 a watan Afirilun 2014.

Bayan nan ne mayakan kungiyar Abubakar Shekau suka shiga kungiyar IS, amma kuma kawancen ya kasance mai tangal-tangal.

Kungiyar IS ta sauke shi daga kujerar shugabancin kungiyar ta maye gurbinsa da Abu Mus'ab al-Barnawi.

Masharhanta da dama sun yi imanin Shekau- wanda yanzu ake raderadin cewa bai da lafiya- an sauke shi daga mukamin ne saboda salon da yake amfani da shi ciki har da tura yara kanana su kai hare-haren kunar bakin wake da bama-bamai barkatai ciki har da a wuraren ibada.

Cikin kimanin shekaru uku da suka gabata, dakarun Najeriya sun sake kwato galibin yankunan da mayakan ke iko da su, kodayake dai bangarori biyu na kungiyar na ci gaba da kai hare-hare.

Hare-hare da motocin yaki

To amma tasirin kungiyar IS na karuwa, kuma mai sharhi kan lamuran tsaro Abdullahi Yalwa ya yi imanin cewa wasu daga cikin masu tayar da kayar baya na kungiyar ta ISWAP, mai yiwuwa ana horar da su ne a wajen Najeriya.

ISWAP ce ta kai hare-hare da dama na rashin tsoro wadanda suka yi sanadiyyar hasarar rayuka cikin watanni hudu da suka gabata.

Sukan kai hare-haren ne cikin jerin motoci masu dauke da bindigogi kiri da muzu, inda suka yi hakon wuraren da sojoji su ke zama, ga alama domin samun karin makamai da manyan motoci masu sulke da kuma haddasa hasarar rayuka.

Ita kuwa rundunar sojin Najeriya mai zurfin ciki, ba ta bayyana adadin sojojin da ake kashewa ga alama saboda fargabar hakan zai iya sanyaya gwiwar sojoji da ke yaki da masu tayar da kayar bayan.

Wadannan hare-haren suna kuma sanya shakku kan daya daga cikin manyan alkawuran da shugaba Muhammadu Buhari ya yi lokacin da ya hau karagar mulki a 2015 wato na cewa zai murkushe kungiyar Boko Haram.

Yanzu kuma ana ci gaba da nuna damuwa game da matsalar tsaro a Najeriya gabanin sabbin zabuka da ake shirin yi a watan Faburairun 2019 lokacin da shugaba Buhari ke son a sake zabensa domin wa'adin mulki na biyu.

Malam Abdullahi Yalwa ya ce abubuawa uku ne ke haddasa hare-haren Boko Haram:

  • Kasuwanci- wato wadanda ke amfani da rikicin Boko Haram domin samun kudi.
  • Akida- mayakan da ke shiga saboda an cusa masu mummunar akida ta addini.
  • Siyasa- mayakan da ake jin wasu 'yan siyasa na basu kudi domin rura wutar fitinar a yunkurin bakanta wadanda ke mulki.

Ya kara da cewa yayin da har yanzu dubban 'yan gudun hijira sanadiyyar rikicin ba su koma gidajensu ba, batun tsaro na ci gaba da kasancewa wani babban al'amari na yakin neman zabe.

'An kashe Kwamandan mayaka mai sassauci.'

Bangarori biyu na kungiyar ta Boko Haram dai na ayyukansu ne a sassa daban-daban na arewa maso gabashin Najeriya. Bangaren kungiyar Shekau galibi sun fi karfi a wajen dajin Sambisa da wasu yankunan iyaka da Kamaru.

Ita kuma kungiyar ISWAP ana jin tana da mazauni ne a yankunan iyaka da Nijar, ko da yake dukkanin kungiyoyin biyu na wadari a kewayen tafkin Chadi.

Bayan rarrabuwar kungiyar Boko Haram an samu rahotannin cewa bangarorin sun yi ta kafsa fada a tsakaninsu inda aka samu hasarar rayuka, lamarin da ya taimaka wa sojoji wajen yaki da masu tayar da kayar bayan.

A cikin kungiyar ISWAP ma akwai zaman tankiya. An yi imanin wasu mukarraban wani babban kwamanda na kungiyar, Mamman Nur, sun kashe shi, bayan sako 'yan matan Dapchi.

Ana zargin cewa shi ya yi gaban kansa wajen ba da umarnin a sako 'yan matan ba tare da biyan kudin fansa ba.

A cewar jaridar Daily Trust wacce ake ganinta da kima, wannan 'sassaucin' abu ne da mayakan ba su lamunta ba, don haka suka kashe shi a ranar 21 ga watan Agusta.

Idan ta tabbata an kashe shi, to hakan zai iya kasancewa wani dalili na karin tsauri da kungiyar ta yi cikin watanni biyu da suka gabata, da kuma kisan gillar da ta yi wa ma'aikatan agajin, a wani salo irin na kungiyar IS dake Gabas ta Tsakiya.

Abdullahi Yalwa ya ce shigar kungiyar IS cikin rikicin, lamarin da ya kara sanya matsalar tayar da kayar bayan ta kasance mai sarkakiya, da kuma karin dabarar yaki.

'Ana bukatar karin bayanan sirri da kuma gogewa daga bangaren sojoji', domin dakarun tsaron Najeriya su iya dakile matsalar, a cewarsa.

To amma ministan tsaron Najeriya Mansur Muhammad Dan-Ali na da kwarin gwiwar samun nasara, inda a kwanakin baya ya shaida wa BBC cewa daukar karin sojoji 10,000 da kuma horar da su da ake yi duk shekara, da kuma karin kayan aiki da ake samu, za su taimaka wajen samun gagarumar nasara a karshe.

Birtaniya da Amurka dai na bai wa Najeriya tallafi ta fuskar soji, kuma gwamnati na fatan soma samun jiragen yaki samfurin Super Tucano A-29 guda 12 daga kasar Amurka a cikin shekara mai zuwa.

To sai dai kuma, ga al'umomin dake arewa maso gabashin Najeriya lamarin rikicin na ci gaba da daukar lokaci mai tsawo, kuma da wuya a iya fita daga matsalar nan kusa, musamman ganin yadda masu tayar da kayar bayan da kuma sojoji ke kara kaimi a ayyukansu na yaki.