Fafaroma ya bukaci 'yan mafia su daina sabon Allah

Fafaroma Francis ya yi kira ga 'yan kungiyoyin mafia su daina sabon Allah sannan su rika nuna kauna ga jama'a.

Ya yi kiran ne lokacin da yake yin addu'a ga limamin coci Giuseppe Puglisi wanda 'yan mafia suka harbe har lahira a Sicily shekara 25 da suka gabata.

Fafaroma ya gargadi "maza da mata 'yan uwan juna" cewa ba za su yi imani da Allah ba sannan su ci gaba da zama 'yan mafia - hakan wani hannunka-mai-sanda ne ga 'yan mafia wadanda suke bautawa Allah.

Ranar Asabar da safe, Fafaroma ya yi jawabi ga mabiyansa a Piazza Europa da ke Palermo kuma nan gaba kadan ne zai ziyarci wani wurin bauta a Brancaccio.

Fafaroma ya shahara wurin aiki da matasa domin ya kaar da tunaninsu daga barin shan miyagun kwayoyi da shiga kungiyoyin mafia.

Ya ce Sicily na bukatar "maza da mata da ke kaunar juna, ba wadanda ke son raba kan juna ba'".

An harbe limamin Puglisi a kofar gidansa lokacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa, ranar 15 ga watan Satumbar 1993.

Kisan nasa ya faru ne lokacin da kungiyoyin mafia ke tashen rikici da abokan hamayyarsu lamarin da ya sanya fargaba a tsakanin jama'a.