Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe majalisar dokokin Najeriya za ta koma zama?
An dai yi ta matsa lamba ga shugabancin majalisar dokokin Najeriya da su sake bude zauren majalisar domin yin nazari game da wasu muhimman batutuwa na ci gaban kasa.
Wani muhimmin abu da ake ganin ya kamata a duba cikin hanzari shi ne kasafin kudin zaben kasar na shekara ta 2019, wanda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aika wa majalisar kafin ta tafi hutu.
A ranar Talatar da ta gabata ne majalisar dokokin Najeriya ta ce ta so ta zauna domin duba batun na kasafin kudin hukumar zaben kasar INEC.
Sai dai zaman bai yiwu ba, bayan da jami'an hukumar farin kaya DSS suka datse kofar shiga majalisar na wani lokaci.
Amma a ranar Alhamis, majalisar ta ce akwai yiwuwar za ta katse hutunta a mako mai zuwa domin yin nazari game da kasafin kudin zabukan na 2019, wanda aka kasa yi a ranar Talata.
Hakan kuwa ya zo ne bayan wata ganawa tsakanin shugabannin majalisar da shugaban hukumar zaben kasar INEC, farfesa Mahmood Yakubu.
Sanata Isah Hamma Misau, daya ne daga cikin wakilan kwamitin da ke kula da hukumar zabe a majalisar dattijai, kuma su ne za su duba kasafin kudin kafin majalisar ta amince da shi.
Ya ce akwai yiwuwar majalisar ta dawo daga hutu a mako mai zuwa, amma ba a tsayar da takamaimiyar ranar da hakan zai faru ba.