An nada sabon shugaban hukumar DSS

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency
Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya umarci mutumin da ya fi mukami a hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) Matthew B. Seiyefa ya maye gurbin Lawal Daura, wanda aka sallama daga aiki ranar Talata.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta shafinta na Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hakazalika rahotanni a kasar suna cewa mukaddashin shugaban yana ganawa da sabon shugaban hukumar.
Rahotanni sun ce, Mista Seiyefa, mutumin da ya fito daga jihar Bayelsa, ya isa fadar shugaban kasar ne da misalin karfe 4 na yamma rike da wasu takardu a hannunsa.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya fara hutun kwana 10 a kasar Birtaniya.
Abin da ya sa mataimakinsa yake jan ragamar kasar a matsayin mukaddashin shugaba.
Matakin cire Lawal Daura din ya zo bayan wasu jami'an hukumar DSS din sun hana wasu sanatoci shiga majalisar dokokin kasar da safiyar Talata.







