2019: Dalilan da suka sa Saraki fita daga APC

Bukola Saraki

Asalin hoton, Saraki/Facebook

Bayanan hoto, A baya Sanata Abubakar Bukola Saraki ya fita daga PDP zuwa APC yanzu kuma ya sake yiwa PDP din kom

Al'amuran siyasar Najeriya sun shiga wani sabon salo a karshen watan Yuli na bana (2018), zuwa farkon watan Agusta.

Guguwar siyasar ta fara kadawa ne yayin da wasu 'yan majalisun dokokin kasar, da gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, suka bayyana ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki, sannan da dama su suka koma Jam'iyyar PDP ta hamayya.

Yanayin ya kara daukar dumi bayan da shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki da gwamnonin jihohin Kwara Abdulfatah Ahmed da na Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal suka fita daga jam'iyya mai tsintsiya suka koma mai lema.

Mafi yawan 'yan majalisar da suka fice daga APC na cewa, rashin adalcin da jam'iyyar ke nuna musu, da rashin iya mulki, da yadda al'amura ke kara tabarbarewa da rashin tsaro su ne suka sa su daukar matakin.

Dalilan ficewar Saraki daga APC

Alhaji Abdulfatah Ahmed

Asalin hoton, Abdulfatah/twitter

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kwara Alhaji Abdulfatah ahmed na daga wadanda suka fice daga ACP zuwa PDP.

Sanata Bukola Saraki shi ne mutum mafi girman matsayi da ya fice daga APC zuwa PDP.

Sanata Saraki na da dimbin magoya baya da suka bi shi zuwa jam'iyyar PDP, cikinsu har da gwamnan jihar Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmed, da tsohon mai magana da yawun jam'iyyar APC Malam Bolaji Abdullahi, da sanatoci da 'yan majalisun tarayya da na jihar ta Kwara.

Ya bayanna wasu dalilai da suka sanya shi sauya shekar, wanda ya bayyana da cewa mataki ne mai wahalar gaske da ya zama dole ya dauke shi a wannan lokaci.

1. 'Yan hana ruwa gudu

A sanarwar da Saraki ya fitar ya ce akwai wasu 'yan hana ruwa gudu a jam'iyyar ta APC da suka toshe duk wata hanya da za a iya amfani da ita wajen yin sulhu, da samar da zaman lafiya a cikin jam'iyyar ta APC.

Ya yi zargin cewa irin wadannan mutanen sun yu fatali da ka'idojin APC na samar da daidaito, sannan sun yi watsi da dukkan abubuwan da suka kamata a yi wajen tafiyar da jam'iyyar da gwamnati cikin kyakkyawan yanayi.

2. Mayar da mutanensa saniyar ware

Sanata Saraki ya ce a cikin shekaru ukun da jam'iyyar APC ta yi tana mulki, "an mayar da magoya bayansa saniyar ware, ba a yin komai da su, an mayar da su tamkar agololi," a cewar Saraki.

Sannan kuma ya ce wasu mutane da suke juya gwamnati sun hana samun duk wata dama da za a warware wadannan matsaloli.

Wannan layi ne

3. Batawa 'yan majalisa suna

Shugaban majalisar ta dattijan Najeriya ya ce duk da irin kokarin da ya yi wajen bai wa gwamnati kariya a majalisun kasa a matsayinsa na jagoran majalisun, bangaren zartarwa na yi wa duk wani mataki da suka dauka na yin aikinsu kamar yadda doka ta tanada a matsayin kokarin yi wa gwamnati zagon kasa.

Ya ce ana yawan amfani da ikirarin da gwamnati ke yi na cewa tana yaki da cin hanci da rashawa, a shafa musu kashi domin a hana su yin magana.

Saraki ya ce sai da aka yi kulle-kulle aka shiga tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa, aka haifar da rashin yarda da juna.

4. Tura ta kai bango

Bukola Saraki ya ce wani dalilin da ya sa shi barin jam'iyyar ta APC shi ne yadda wasu jagororin jam'iyyar suke yi wa duk wani yunkuri na sulhu-musamman na baya-bayan nan kafar ungulu.

Saraki ya ce yunkurin sabon shugabancin jam'iyyar, da mataimakin shugaban kasa, da wasu gwamnoni na ganin an sulhunta rikice-rikicen da ake fama da su a jam'iyyar, sun sa masa kwarin gwiwar cewa akwai wata damar sasantawa, duk da cewa lokaci ya kure.

To sai dai ya ce wasu da suka yi tsalle suka dire suka tabbatar da cewa sai da aka kure Sarakin da magoya bayansa ba su samu wani farcen susa a cikin jam'iyyar ba.

Ita kuwa jam'iyyar APC ta musanta zarge-zargen da Sarakin ya yi mata da kuma gwamnatinta tana mai cewa tun da man Saraki ba ya tare da gwamnatin jam'iyyar.

Wannan layi ne

Tuni dai Sarakin ya bayyana cewa ya yi wa PDP kome, ma'ana ungulu ta koma gidanta na tsamiya.

Masu fashin baki dai na ganin guguwar sauya shekar daga APC zuwa PDP na iya yi wa jam'iyyar mai mulki mummunan tasiri a zabukan badi, kamar yadda ya yi wa jam'iyyar PDP a zabukan 2015.

Wannan layi ne

Jerin sunayen jiga-jigan da suka sauya sheka zuwa yanzu

sanatoci
  • Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
  • Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal
  • Kakakin jam'iyyar APC Bolaji Abdullahi Ahmed
  • Jakadan Najeriya a Afirka Ta Kudu, Ahmed Ibeto
  • Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom
  • 'Yan majalisar dokoki ta kasa fiye da 50 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP da suka hada da Kwankwaso da Hunkuyi da Melaye da Hamma Misau da Nazif Gamawa da sauran su
  • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i
  • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar
  • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa sun koma jam'iyyar ADC
  • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
  • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.