Ba ka da Ganduje ne a gabanmu ni da Kwankwaso ba – Shekarau
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Tsohon gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce ba kada gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne a gabansu shi da Sanata Rabiu Kwankwaso ba.
A makon jiya ne tsofaffin gwamnonin na Kano biyu suka gana a karon farko cikin shekaru da dama, kwanaki kadan bayan Kwankwaso ya sauya sheka daga APC zuwa PDP inda ya tarar da Shekarau.