Ba ni da niyyar komawa APC – Shekarau

Shekarau

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon Gwamnan Kano kuma jigo a jam'iyyar PDP Malam Ibrahim Shekarau ya ce ba shi da niyyar komawa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Shekarau na mayar da martani ne kan wasu rahotanni da ke cewa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na zawarcinsa zuwa APC.

A ranar Alhamis wasu kafafen yada labarai suka bayar da rahoton cewa jiga-jigan APC a Kano da Abuja sun fara tattaunawa da Malam Shekarau da nufin shawo kansa zuwa jam'iyyar.

Jaridar Daily Trust ta ce lamarin ya karfafa ne saboda sauya shekarar da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda abokin hamayyar siyasar Shekarau ne, ya yi daga APC zuwa PDP.

Sai dai mai magana da yawun tsohon gwamnan Sule Ya'u Sule, ya shaida wa BBC cewa mutanen da jaridar ta ce sun gana da APC ba wakilansu ba ne, kuma ba da yawun tsohon gwamnan suka yi ba.

"Ya ce ba da hannun malam suka yi ba. Wadannan mutane ne da dama can sun raba-gari da Malam Shekarau," a cewar Sule Ya'u.

Ya kara da cewa ba su da "masaniyar" ganawar da aka ce Ganduje ya yi da wasu da ke ikirarin cewa su wakilan Shekarau ne.

Tun bayan da tsohon Gwamna Kwankwaso ya bayyana ficewa daga APC zuwa PDP, masana ke sanya alamar tambaya kan yadda tafiya za ta kasance tsakaninsa da Malam Shekarau.

Manyan 'yan siyasar biyu sun dade suna hamayya da juna tun shekarar 2003 lokacin da Shekarau ya kayar da Kwankwaso a zaben gwamnan jihar.

Daga bisani kuma Kwankwaso ya sake yunkurowa ya kwace mulkin bayan Shekarau ya kammala wa'adinsa a shekarar 2011.

Wata majiya mai karfi a bangaren Kwankwaso ta shaida wa BBC cewa tsaffin gwamnonin biyu na da kyakkyawar fahimta da juna a yanzu, kuma nan gaba kadan za su hadu.

Masu sharhi na ganin idan har mutanen biyu suka yi aiki tare to za su iya zama babban kalubale ga jam'iyyar APC a Kano.

Wadanda suka fice daga APC a kwanan nan

Bayanan sautiJam'iyyar APC ta kauce hanya - Buba Galadima
  • 'Yan majalisar dokoki ta kasa 51 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP
  • Gwamnan Benue Samuel Ortom da 'yan majalisar jihar da dama
  • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i
  • Suna dai samun goyon bayan Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi
  • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar
  • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa
  • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
  • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.
Presentational grey line