Sauya sheka: Buhari ya yi wa su Kwankwaso fatan alheri

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani game da batun sauya sheka da wadansu 'yan majalisar dokokin kasar fiye da 50 suka yi zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.
Shugaban ya ce yana yi wa 'yan majalisar fatan alheri. Kuma ya bukaci sauran 'yan jam'iyyar kada su karaya bayan faruwar hakan.
Ya ce jam'iyyar ta yi kokarin hana masu sauya shekar, "kuma wajibi ne na yaba wa kokarin shugabancin jam'iyyar game da yadda ya rika aiki ba dare, ba rana don hada kan jam'iyyar da kuma daidaita al'amarin don samun nasara a nan gaba," kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Daga nan ya ce ka da gwiwar sauran 'yan jam'iyyar APC ta yi sanyi, inda ya ce an saba ganin irin haka idan ana tunkarar babban zabe.
"Na fahimci cewa wadansu 'yan majalisar sun samu rashin jituwa ne da rassan jam'iyyar da ke jihohi, ko yankunansu musamman game da batun karba-karba wanda ya hana wadansunsu damar sake dawowa majalisar," in ji Shugaba Buhari.
Hakazalika shugaban ya ce babu wani daga cikin 'yan siyasar da suka sauya sheka da "yake da matsala da shi ko gwamnatin da yake jagoranta. Kuma ni ma babu wani cikinsu da nake da matsala da shi."
Ya ce yana mutunta 'yancinsu na zabar duk wata jam'iyya da suka yi ra'ayi.
A karshe ya ce a shirye yake ya yi aiki da majalisar dokokin kasar da mambobinta duka, "ba tare da la'akari da jam'iyyarsu ba."

Ba mu ji dadin abin da ya faru ba - APC
A nata martanin, jam'iyyar APC mai mulkin Najeriyar ta ce ba ta ji dadin yadda wasu 'ya'yan nata suka sauya sheka ba.
Mai magana da yawun jam'iyyar Bolaji Abdullahi ya shaida wa BBC cewa sun yi iya kokarinsu domin ganin ba a kai ga wannan mataki ba, amma ba su yi nasara ba.
"Za mu ci gaba da daura damara domin tunkarar abin da zai biyo baya," a cewarsa.
Ya kara da cewa har yanzu mu ke da rinjaye a majalisar wakilai, da kuma yawan gwamnoni.
Da aka tambaye shi kan ko 'yan majalisar za su yi yunkurin tsige Shugaba Buhari, sai ya ce:
"Ba na zaton haka zai yi wu domin abu ne mai wuya. Ko Amurka ma bai taba faruwa ba."

PDP ta yi maraba da su
Jam'iyyar PDP ta yi maraba da sabbin 'ya'yan da ta samu sakamakon sauyin shekar da aka samu a majalisar dokokin kasar.
Mai magana da yawun PDP Kola Ologbondiyan ya shaida wa BBC cewa suna maraba da bakin nasu.
"Wannan wani babban ci gaba ne ga tafarkin demokuradiyyar Najeriya," a cewarsa.
Ya kara da cewa hakan zai ba su damar tserar da kasar daga manufofin "kama-karya na Shugaba Muhammadu Buhari" da kuma bai wa jama'ar kasar mulki mai inganci.











