Salah ya yi bankwana da Rasha 2018

Asalin hoton, Getty Images
Shahararren dan wasan kasar Masar Mohamed Salah ya yi bankwana da gasar cin kofin duniya bayan kasarsa ta buga wasan karshe da Saudiyya a ranar Litinin.
Saudiyya ta doke Masar ne da ci 2-1 a ranar Litinin - duka kasashen biyu sun fita daga gasar ke nan bayan buga wasanni uku a matakin rukuni.
Rawar da dan wasan Masar da Liverpool ya taka a kakar da aka kammala ta ja hankalin duniya, kuma ta sa an yi hasashen zai taka rawar gani a gasar kofin duniya.
Mohamed Salah ne ya fi kowa cin kwallo a gasar Firimiya da aka kammala, kuma shi ne ya jagoranci kasarsa zuwa Rasha bayan shafe shekara fiye da 20 ba su yi hakan ba.
Sai dai bayan da rauni ya hana shi buga wasan farko da kasar ta yi da Uruguay, fitaccen dan kwallon zai yi bankwana da gasar ta Rasha 2018.
Kwanaki kafin a fara gasar ne dan kwallon ya ji rauni a kafadarsa a wasan karshe na gasar Zakarun Turai tsakanin Real Madrid da Liverpool.
Lamarin da ya sa shakku a kan ko ma zai iya halartar gasar baki daya.
A karshe dai ya samu ya halarci gasar amma bai buga wasan da Masar ta sha kashi a hannun Uruguay da ci 1-0 ba, kuma wasu na ganin rashinsa ya yi wa tawagar illa.
Salah ya buga wasa na biyu da Rasha ta doke Masar da ci 3-1, inda ya ci kwallo daya tilon da suka zura ta bugun fanareti, sai dai hakan bai wadatar ba.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan rashin nasarar a hannun masu masaukin baki, ita ce ta kora Salah tare da tawagar Masar gida.
Sai dai wasan karshe da za a fafata tsakanin Masar da Saudiyya shi ne zai zamo na karshe da Salah zai buga a gasar ta bana kafin ya koma gida.
Wasan dai ba shi da wani tasiri ta fuskar zuwa zagaye na biyu ko akasin haka, domin an riga an fitar da duka kasashen biyu daga gasar.
Masu sha'awar kwallo da kuma goyon bayan Salah za su so su ga ya taka rawar gani a wasan domin yin ban kwana da gasar cikin wani yanayi mai burgewa - musamma ma saboda kasarsa ba ta taba samun nasarar cin wasa a tarihin gasar.
Sai dai duk abin da zai yi a wasan na Saudiyya, ba zai kawar da bakin cikin fitar da su daga gasar a zagayen farko ba.
Haka kuma ba lallai ba ne ya share wa magoya bayansa hawayen rashin ci gaba da ganinsa a gasar ba.










