Kalli yadda 'yan Najeriya ke shirya wa Argentina

Wasan shi ne zai tantance makomar kasashen biyu a gasar ta Rasha 2018, kuma hankalin duniya ya karkata a kansa.

'Yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto, Wannan wasa shi ne babban kalubale da 'yan wasan Super Eagles za su fuskanta kawo yanzu tun bayan fara gasar
'Yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto, Masana da yawa na hasashen Najeriya za ta sha wuya a wasan, amma wasu na ganin Eagles za su iya kai labari saboda Argentina ba ta taka-leda sosai ba a wasanninta na baya
'Yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto, Ahmed Musa wanda shi ne ya ci kwallo biyun da Najeriya ta doke Iceland da su, ya na cikin 'yan kwallon da su ka yi atisaye
'Yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto, Dan wasan baya Leon Balogun na daga cikin wadanda suka yi atisaye, kuma ana sa ran zai taka-leda a wasan
'Yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto, 'Yan wasan na Najeriya sun ce sun shirya tsaf domin tunkarar tawagar Argentina wacce ta kunshi manyan 'yan wasa irinsu Messi da Aguero
'Yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wajibi ne Argentina ta ci Najeriya idan har tana so ta kai zagaye na gaba saboda maki daya ne da ita tal bayan wasa biyu da ta yi.
'Yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ita kuwa Najeriya za ta iya kai labari idan aka tashi canjaras idan har Iceland ba ta iya cin Croatia ba
'Yan wasan Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan kwallon na Super Eagles na atisaye tukuru, kuma tuni suka isa birnin St Petersburg inda anan ne za a fafata wasan da misalin karfe 07.00 na yamma agogon Najeriya