Najeriya za ta rufe iyaka saboda shigo da 'shinkafa mai guba'

Hukomomi a Najeriya sun ce za su rufe iyakokinsu da wata kasa makwbciya da ba a bayyana sunanta ba nan da kwanaki kadan masu zuwa domin hana shigo da shinkafa daga kasashen waje ta bayan fage.

Ministan ma'aikatar noma na Najeriya Audu Ogbeh, ya ce: "Akwai abubuwa masu guba da ake sakawa a cikin shinkafar" kuma akwai sinadarin "arsenic", ya kuma yi ikirarin cewa daga China da kuma kudu maso gabashin Asiya ne ake shigowa da shinkafar cikin Afirka.

Ministan ya ce yana da kwarewa sosai kan maudu'in saboda "shi ne manomi na farko da ya sassake shinkafa ba tare da tsakuwa ba."

Ya kara da cewa: "A nahiyar kudu maso gabashin Asiya inda ake suke shinkafa, idan ka yi shekara hudu zuwa shida kana shuka shinkafa a wuri guda babu kakautawa yawan sinadarin arsenic zai ci gaba da karuwa.

"Sinadarin Arsenic na kawo cutar sankara kuma wannan shi ne abin da suke jibge mana. Wasu mutane sun ce sun fi son shinkafar kasar Thailand saboda tana da tsafta . Amma fa tana da guba!"

Ko da yake hukumomin Najeriya ba su bayyana sunan kasar da ake shigo da shinkafar ta kan iyakarta ba, amma kafofin watsa labarai na cikin gida sun dora alhaki kan Jamhuriyar Benin.

Najeriya na cikin kasashen Afirka da su ke son su kara yawan shinkafar da suke samarwa a cikin gida.

A cikin kasashe 39 masu samar da shinkafa a Afirka, 21 daga cikinsu na shigo da kashi 50 da kashi 99 na shinkafar da suke bukata a cikin gida, a cewar hukumar abinci da aikin noma ta Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarar 2017 ne ministan noman ya yi ikikarin cewa Najeriya za ta samar da shinkafar da za ta iya ciyar da kanta, sai dai wasu masana sun bayyana matakin a matsayn "mafarki".