Najeriya da Ghana ne inda aka fi zub da ciki a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Yadda ake bincike game da kwayoyin zubar da ciki a Google ya nunka a shekaru 10 da suka gabata, kamar yadda wani binciken da BBC ta gudanar ya nuna.
Sakamakon binciken kuma ya gano cewa an fi yin binciken kwayoyin a intanet a kasashen da aka haramta zubar da cikin.
Mata sun koma bin hanyoyi na fasaha domin zubar da ciki ta hanyar sayen kwayoyin a intanet da yada bayanan likita ta kafar Whatsapp.
Yanzu wannan ake kira hanyar zubar da ciki ta zamani.
Kasashen da aka tsaurara dokoki, inda sai don a ceto rayuwar mace ake zubar da ciki ko kuma inda aka haramta baki daya, an fi binciken kwayoyin zubar da cikin a intanet fiye da kasashen da babu wata doka.
Hanyoyi biyu ne ake a bi wajen zubar da ciki: Tiyata da magani.

Zubar da ciki ta hanyar shan magani ya shafi shan nau'o'in magungunan Misoprostol da Mifeprostone, wadanda idan an sha zai sa ciki ya zube.
Kamar a Birtaniya, likitoci ne ke rubuta magungunan, yayin da kuma matan da ke bincike a intanet a kasashen da aka takaita zubar da ciki, suke keta doka, inda za su iya fuskantar hukunci.
Ghana da Najeriya ne kasashe biyu da aka fi binciken kwayar Misoprostol, kamar yadda alkaluman Google suka nuna.
A Ghana ana bayar da damar zubar da ciki ne idan an yi wa wata fyade ko kuma don kokarin ceto rayuwar wata.
Haka ma a Najeriya, dokar kasar ta bayar da damar zubar da ciki ne kawai idan an ga rayuwar mace na cikin hatsari.
Daga cikin kasashe 25 da aka fi binciken maganin zubar da ciki na Misoprostol, kasashe 11 daga Afirka ne yayin da 14 kuma daga Latin Amurka.
Dukkanin kasashen sun haramta zubar da ciki ko kuma sun yarda ne kawai a zubar da ciki a lokacin da rayuwar mace ke cikin hatsari.
Zambiya da Mozambique ne kawai daga cikin kasashen da ba su haramta zubar da ciki ba.

A Ireland, hukuncin shekaru 14 a gidan yari ake yanke wa duk wadda ta zubar da ciki ta hanyar shan kwayoyi, ko da yake sakamakon kuri'ar raba gardama da aka gudanar a watan Mayu ya nuna 'yan kasar na son a soke dokar.

Alkaluman Google ba wai kawai sun nuna kasashen da aka fi binciken magungunan zubar da ciki ba. Sun kuma nuna kalmomin da ake yawan amfani da su a kan maudu'i daya.
"Kwayoyin zubar da ciki" ne aka fi amfani da su wajen bincike a mafi yawancin kasashen da BBC ta gudanar da bincike akai.
"Yadda za a zubar da ciki" wannan ce tambayar da aka fi yawan tambaya a kasashen.
"Yadda za a yi amfani da Misoprostol, Farashin Misoprostol, sayen Misoprostol da yadda za a sha Misoprostol, su ne kalmomin da aka fi amfani da su a wajen binciken batun zubar da ciki.

Ana kuma yawan binciken magungunan gargajiya na zubar da ciki a intanet.
A yayin da kuma ake binciken kwayoyin zubar da ciki, mata kuma na amfani da Google domin binciken hanyoyin da mutum zai bi da kansa don zubar da ciki.
"Yadda za a zubar da ciki a gida" ne aka fi bincike a Google.
Yadda babu cikakkun bayanai da suka shafi kare lafiya, binciken ya nuna cewa abu ne mai wahala a iya kiyaye adadin maganin da ya kamata a sha da kuma illolinsa.
Babu daya daga cikin hanyoyin zubar da ciki na gida a jerin hanyoyin zubar da cikin da suka dace na Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.

Asalin hoton, Getty Images
A duniya, ana zubar da ciki sau miliyan 25 a hanyoyin da ba su dace ba duk shekara, a cewar WHO.
Duk da cewa amfani da Misoprostol ana daukarsa hanyar zubar da ciki da ta dace idan kwararre ne ya bayar da umurnin amfani da maganin, amma akwai barazana idan ba a bi tsarin da ya kamata ba.
"Ko da a ce maganin yana da kyau kuma an bi umurnin likita, ana iya samun matsala," in ji Dhammika Perera, darakta a Marie Stopes International.
Idan mace ta sayi maganin a intanet, ko kuma daga likitan da ba kwararre ba, yana kara damar zubar da ciki a hanyar da ba ta dace ba, in ji shi.
Yana da wahala wadannan matan su tafi asibiti a duba lafiyarsu idan har sun zubar da ciki a hanyar da ba ta dace ba.
Kunya da tsada da rashin wadatuwar wuraren shan magani ne matsalolin da matan ke fuskanta, a cewar Mista Perera.

A kwanan nan BBC ta saurari labarin Arezoo, dalibar nazarin ilimin shari'a da ke Iran, lokacin da ta gano tana dauke da juna biyu na saurayinta da suke rayuwa shekaru biyar.
Sun dade suna amfani da kwayoyin hana daukar ciki.
"Duk wani ofishi na likitan mata da na gani sai na shiga" in ji ta.
"Duk lokacin da likitoci suka duba ni kuma suka fahimci cewa ba ni da aure zan zubar da ciki, nan take suke watsi da ni."
Ta yi takardun karya cewa ita bazawara ce domin samun amincewar likita ya taimake ta.
Arezoo ta shiga intanet inda ta ci karo da wata kungiya da ke bayar da maganin zubar da ciki ga mata a kasashen da aka haramta zubar da ciki. A nan ne ta samu taimako da shawarwari.
Maganin da ta karba daga hannun likita ya sa ta yi ta zubar da jini, lamarin da ya sa aka ruga da ita zuwa wani asibiti mai zaman kansa tare da rakiyar 'yar uwarta.
"Na yi ma su karya cewa mijina yana Faransa kuma na manta inda na ajiye takardu a wani wuri kuma ina son na zubar da ciki ta hanyar da ta dace."
Jami'an asibitin dai ba su gamsu ba kuma sun ki ba ta gado.
Arezoo ta ce kamar wani abin al'ajabi, daga baya sun amince da ita.
"Duk da labarin karyar da na shirya, an kwantar da ni a asibiti, kuma cikin minti 30 aka kammala aikin. Wannan shi ne lokaci mafi muni a rayuwata," a cewarta.

Kusan kashi 14 na zubar da cikin da ake yi, ana bin matakan da ba su dace ba, wanda ke nufin ana bin matakai ne masu hatsarin gaske.
Wasu matsaloli na cututtuka kan biyo baya da kuma matsalar zubar da cikin da ba a kammala ba a irin wannan tsarin.
Idan har ba a yi sa'ar zubar da ciki da kyau ba, kwararren likita kan bayar da shawarwari na wasu magunguna ko kuma tiyata, ya dai danganta da yanayin matsalar.
A kalla mata 22,800 ke mutuwa duk shekara sakamakon rashin sa'ar zubar da ciki da kyau, kamar cibiyar Guttmacher ta ruwaito.
Wadanda suka tsara rahoton: Amelia Butterly da Clara Guibourg da Dina Demrdas da, Nathalia Passarinho da kuma Ferenak Amidi.


Mene ne shirin mata 100?
A ko wacce shekara shirin BBC na mata 100 yana fitar da mata 100 wadanda suka yi fice ta hanyar tasiri da kwarjini a sassan duniya.
A shekarar 2017, mun kalubalance su da su warware matsaloli hudu da suka fi addabar mata a yau a sassan duniya - matsalar da ke hana ci gaban mata da rashin karatun mata da muzguna wa mata a wuraren taron jama'a da kuma nuna wa mata bambanci a harkar wasanni.
Da taimakonku, za su samar da hanyoyin magance matsalolin, kuma muna son ku ba da naku hanyoyin magance matsallolin ta shafukan Facebook da Instagram da kuma Twitter. Ku yi amfani da maudu'in #100Women.











