Wai me Obasanjo ke tsoro da gwamnatin Buhari ne?

Cif Olusegun Obasanjo
Bayanan hoto, Dangantaka ta yi tsami sosai tsakanin Cif Obasanjo da Muhammadu Buhari
    • Marubuci, Umar Shehu Elleman
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Lagos

Kusan za a iya cewa a yanzu Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo na kan gaba a sahun mutanen da ke adawa da gwamnatin Muhammadu Buhari, kuma suke kokarin ganin bayanta. Sai dai wasu na sanya almar tambaya kan ainahin manufar tsohon shugaban.

A 'yan makonnin da suka wuce ne Obasanjo ya kai ziyara ga shugabannin kungiyar Yarbawa ta Afenifere domin duba yadda "za a sauya gwamnatin Shugaba Buhari, wacce ya ce tana neman jefa kasar cikin wani hali na tsaka mai wuya".

Sai dai ganin yadda ziyarar ta zo a lokacin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin tsohon shugaban da kuma gwamnatin APC, wasu na ganin akwai lauje a cikin nadi.

Amma Obasanjo, wanda ya goyi bayan Buhari a zaben 2015, ya nuna ba shi da abin da za a zarge shi da shi, illa dai ziyarar ta neman ceton kasar ce.

Kalaman da Buhari ya yi na shagube a kan yadda aka kashe makudan kudade kan wutar lantarki a lokacin mulkin Obasanjo "ba tare da an gani a kasa ba" sun sa wasu na hasashen cewa shugaban na da niyyar daukar mataki kan lamarin.

Kwatsam kuma ana cikin haka, sai Obasanjo ya fitar da sanarwa yana zargin cewa gwamnati na shirin amfani da shaidun boge domin kama shi da shafa masa laifi ta karfi da yaji.

Sai dai gwamnatin ta hannun ministan sadarwa Lai Mohammed, ta ce mai kashi a gindi ne kawai zai tsorata, kuma shi mara gaskiya ko a ruwa gumi yake yi.

Tsohon shugaban ya dade yana takun saka da kungiyar ta Afenifere, kuma daga dukkan alamu akwai babban kalubale a gabansa na ganin ya shawo kanta domin cimma manufarsa.

Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa kuma mamba a kngiyar wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida min cewa ba za su saki jiki da Mr Obasanjo ba.

"Duk da cewa muna da matsalolinmu da gwamnatin Buhari, ba mu san manufar Obasanjo ba kuma ba za mu saki jiki da shi ba tukunna," a cewarsa.

Me Obasanjo ke tsoro?

Wasu majiyoyi kuma sun yi zargin cewa Obasanjo na kamun kafa ne ga kungiyar domin ta mara masa baya idan har Shugaba Buhari ya yanke shawarar bincikar gwamnatinsa kamar yadda wasu kungiyoyi ke kiran da aka yi.

Kuma ba za a iya watsi da masu wannan ra'ayi ba ganin kalaman Obasanjo na baya-bayan nan ka cewa ana shirin kama shi, duk da cewa babu wata hujja mai kwari da ya bayar.

Buhari da Obasanjo
Bayanan hoto, Obasanjo na sukar gwamnatin Buhari a kan rashin iya mulki duk da cewa ya goyi bayansa a 2015

Wannan ne ya sa wasu ke zargin cewa Obasanjo na tsoron matakin da Buhari ka iya dauka a kansa ko kuma kan wasu matakai da gwamnatin ta dauka a baya, shi ya sa yake kokarin ganin bayan gwamnatin.

Sai dai shi mutum ne da ya yi kaurin suna wurin juyawa gwamnatoci baya kamar yadda ya yi wa marigayi Umaru 'Yar'adua da kuma Goodluck Jonathan.

Kuma ya nace cewa yana gwagwarmaya ne domin ganin an ceto kasar, saboda a cewarsa Buhari ya gaza ta fannoni da dama.

Sai dai gwamantin ta ce badakalar da Obasanjo da sauran gwamnatocin PDP suka yi ne suke kokarin gyarawa, kuma kawo yanzu an fara samun ci gaba.

Kawo yanzu dai 'yan kasar na zuba ido su ga yadda wannan lamari zai kaya.

Ko Obasanjo zai yi nasara wurin ganin karshen gwamnatin Buhari, ko kuma jam'iyyar APC za ta yi galaba wurin karya tasirin tsohon shugaban a siyasance.

Kuma ko abin da Obasanjo ke tsoro zai faru ganin yadda Buhari ya sha alwashin yakar cin hanci da rashawa, duk da cewa wasu na ganin binciken Obasanjo kamar wani abu ne da shugaban ba zai so ya yi ba?

line

Sabanin Obasanjo da Buhari

Obasanjo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Obasanjo ya mulki Najeriya a matsayin zababben shugaba daga 1999 zuwa 2007
  • Obasanjo ya goyi bayan Buhari a zaben 2015
  • A watan Janairun 2018 ne Obasanjo ya bukaci Buhari kada ya nemi wa'adin shugabanci na biyu
  • Obasanjo ya ce Buhari ya gaza inda ya bukaci ya sauka cikin mutunci bayan wa'adinsa na farko
  • A martaninta, gwamnatin Buhari ta ce ba za ta iya muhawara da Obasanjo ba
  • Ministan watsa labaria Lai Mohammed ya ce idon Obasanjo ya rufe ga nasarorin gwamnatin Buhari
  • Buhari da Obasanjo sun hadu a taron Tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa na Habasha a ranar 28 ga Janairu
  • A watan Afrilu Obasanjo ya jaddada cewa Buhari ya gaza wajen ciyar da Najeriya gaba.
  • Obasanjo ya ce bai kamata a sake zaben Buhari ba saboda gazawarsa.
  • Obasanjo ya kafa wata kungiyar siyasa bayan ya caccaki gwamnatin Buhari
  • A ranar 22 ga Mayu Buhari ya soki gwamnatin Obasanjo kan lantarki
  • Buhari ya ce wani tsohon shugaban kasa ya kashe dala biliyan 16, kuma har yanzu ba lantarki
  • Obasanjo ya mayar wa Buhari da martani a ranar 22 ga Mayu
  • Obasanjo ya ce gwamnatin Marigayi Umaru 'Yar'adu ta kafa kwamitin bincike, kuma kwamitin ya wanke shi.