Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An ci tarar wani yaro naira biliyan 12 saboda ya tada gobarar daji
Wani alkali ya umarci wani yaro ya biya fiye da dala miliyan 36 (£27m) bayan ya amince shi ne ya tada wata mummunar gobarar da ta kwashe tsawon watanni tana ci a jihar Oregon a kasar Amurka.
Alkalin Kotun Jihar Hood River John Olson ya yanke hukuncin cewa dole sai yaron ya rubuta wasikar neman gafara ga mutane 152 wadanda suka makale a hanyan lokacin da gobarar take ci.
Gobarar wadda aka wa lakabi da Eagle Creek ta rika ci har tsawon kusan watanni uku a gundumar Columbia River Gorge, yayin da ta cinye gidaje da yawa.
Lauyan yaron ya bayyana adadin da "ba daidai ba" da wani abu na"rashin tunani".
A watan Fabrairun, yaro mai shekara 15 - wanda ba a ambaci sunan shi ba lokacin zaman kotun- ya amince cewa ya jefa wani abin wasan wuta a ranar 2 ga Satumba 2017 cikin wani busashen rami da ke Eagle Creek Canyon - kimanin mil 50 (80km) daga Portland.
Abin da ya yi ne ya jawo gobara wanda ta ci Eka 48,000, kuma 'yan kashe gobara suka kashe kimanin $18m wurin kashe gobarar.
An yanke masa hukuncin je ka gyara halinka har tsawon shekara biyar, inda zai yi aikin al'umma na tsawon sa'a 1,920 a wani daji da ke kasar Amurka.
Kotun ta amince da cewa yaron ba zai iya biya kudin da aka ci shi tara ba tashi guda.