Cuba: Fiye da mutum 100 sun halaka a hatsarin jirgin Cuba

Asalin hoton, AFP
Fiye da mutane 100 ne suka mutu bayan da wani jirgin sama kirar Boeing 737 ya fado kusa da filin jirgin sama na Jose Marti International da ke Havana, babban birnin kasar Cuba.
Mutum uku sun tsira da rayukansu amma suna cikin wani mawuyacin hali, kamar yadda jaridar kwaminisanci 'Granma' ta ruwaito.
Jirgin na dauke da fasinjoji 104 da kuma ma'aikatan jirgin guda tara.
Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel ya ziyarci wurin da jirgin ya fadi, kuma ya bayyana hadarin a matsayin abin jimami:
"Wannan hadarin abin tayar da hankali ne. Da alama babu mutane da yawa wadanda suka tsira da rayukansu."
Tashar talabijin mallakin gwamnatin kasar ta ce jirgin ya taso ne daga babban birnin kasar zuwa birnin Holguin a gabashin tsibirin.

Asalin hoton, AFP/Getty Images







