Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan sanda na amfani da karfi a kan 'yan shi'a - Amnesty
Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta zargi 'yan sandan Najeriya da amfani da karfi fiye da kima wajen tunkarar mabiya mazahabar Shia da ke zanga-zanga a birnin Abuja
Masu zanga-zangar na neman a sako jagoransu, Sheikh ibrahim el-Zakzaky lokacin da suka yi arangama da 'yan sanda.
Kungiyar Amnesty International ta bayyana yadda 'yan sanda ke tunkarar masu zanga-zangar da harsasai na gaske, da mesar feshin ruwa da kuma hayaki mai sa hawaye, a matsayin mummunan ganganci.
A cikin wata sanarwa, kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta ce wani abin damuwar kuma shi ne yadda jami'an tsaro ke kama dumbin mutane a yayin zanga-zangar.
Kungiyar ta ce kamata ya yi hukumomin Najeriya su mutunta doka kana a saki jagoran na kungiyar 'yan uwa musulmi, kuma ka da su tsangwami masu zanga-zangar lumana.
Arangama da aka yi ta yini biyu tsakanin mabiya shia masu zanga-zangar neman a sako jagoranmsu, da kuma jami'an tsaron kasar, ta yi sanadiyyar raunata gwammman mutane daga bangarorin biyu.
Rundunar 'yan sandan Najeriya dai ta zargi masu mazahabar da soma tayar da fitina ta hanyar jefar farar hula wadanda ba su ji ba su gani ba, da kuma jami'an tsaro da duwatsu.
Mabiya mazahabar Shi'ar sun bayyana cewa za su ci gaba da zanga-zangar har sai an sako shugabansu Sheikh ibrahim el-Zakzaky, to amma ya zuwa yanzu dai koma ya lafa.
Shi dai Sheikh ibrahim el-zakzaky an kama shi ne a 2015 lokacin wani samamen soji da ya yi sanadiyyar kashe mabiyansa fiye da 300 a birnin Zaria.
Sojoji sun zarge su da tare hanya da kuma yunkurin kashe shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya.
Mabiya shi'ar dai na musanta zargin.
Kawo yanzu dai ba a tuhumi malamin addinin a gaban kotu ba
Haka kuma tun bayan kama shi, sau daya aka ganshi a bainar jama'a a cikin watan Janairun bana, lokacin da jami'an tsaro suka fito da shi ya gana da manema labarai, inda ya bayyana cewa ya yi fama da bugun jini.