Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan sanda sun tarwatsa gangamin 'yan Shi'a a Abuja
Jami'an tsaron Najeriya sun yi amfani da karfi wurin tarwatsa mabiya Shi'a da ke zanga-zanga a Abuja, babban birnin kasar.
Wadanda suka shida lamarin sun ce 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye (Tear gas) wurin korar masu gangamin.
Wakilin BBC da ya ziyarci wurin ya ga gwangwanayen hawaki mai sa hawaye a warwatse a wurin da lamarin ya faru.
Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a wasu shafukan sada zumunta sun nuna mabiya Shi'a suna jifan motar 'yan sanda wacce ita kuma ta rinka watsa musu ruwa.
Kawo yanzu rundunar 'yan sandan ba ta ce komai ba kan wannan batu.
Mabiya Shi'ar na wannan zanga-zangar ne a ci gaba da yunkurinsu na tilastwa gwamnati ta sako jagoransu na Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
Wani mabiyin Shi'a ya shaida wa BBC cewa an harbe shi tare da wasu 'yan Shi'ar da dama, sannan ya musanta cewa sun jefi jami'an 'yan sanda.
Ya kara da cewa jami'an tsaro sun yi awangaba da wasu daga cikin mabiyan nasu, sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar wa da BBC hakan.
Wannan lamari shi ne na baya-bayan nan a taho-mu-gamar da ake yi tsakanin jami'an tsaron da mabiya Shi'ar.
A ranar Juma'ar da ta gabata ma 'yan sanda sun kama wani mutum da suka bayyana a matsayin wanda yake shirya zanga-zangar da 'yan Shi'ar suka dade suna yi a dandalin Unity Fountain da ke Abujar.
Wani da ya shaida lamarin ya wallafa hotunan hargitsin a shafinsa na Twitter yana mai cewa: "Masu zanga-zanga da yawa na sake taruwa".
Sannan ya wallafa bidiyo yana mai cewa: "Hayaki mai sa hawaye da karar bindiga kawai ka ke ji".