''Yan daba sun sace' sandar majalisar dokokin Najeriya

Sandar ita ce alamar iko a majalisa a Najeriya

Asalin hoton, Nigerian Senate

Bayanan hoto, Sandar ita ce alamar iko a majalisa a Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya ta ce wasu 'yan daba sun shiga zauren majalisar a ranar Laraba suka kuma sace sandar majalisar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya fitar, ta yi zargin cewa 'yan dabar sun shiga majalisar ne karkashin jagorancin Sanata Ovie Omo-Agege, inda suka sace sandar, wadda ita ce alamar da ke nuna kimar majalisar.

Sanarwar ta bayyana wannan al'amari da cin amanar kasa, "don hakan tamkar kokari ne na kawar da wani reshe na gwamnatin tarayya da karfin tuwo, don haka dole a dauki duk matakin da ya dace.

Tuni dai an kawo wata sandar ta wucin-gadi an ajiye, kuma majalisar ta bai wa Sufeto Janar na 'yan sanda da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, su nemo sandar a cikin sa'a 24, sannan su kamo wadanda suka sace sandar.

Kawo yanzu Sana Omo-Agege, wanda aka dakatar da shi a makon da ya gabata, bai ce komai ba game da zargin da majalisar ta yi masa na shiga da 'yan daba.

Jaridar intanet ta Premium Times ta ruwaito cewa al'amarin ya faru ne 'yan dakiku bayan da Sanata Omo-Agege ya shiga majalisar, inda 'yan dabar da yawansu ya kai 10 suka sace sandar suka kuma tsere.

senate

Asalin hoton, Senate

Jaridar ta ce daga bisani 'yan dabar sun fice daga majalisar a wata bakar mota kirar Jip.

Sanata Sabi Aliyu ya kuma ce wannan abu ci fuska ne ga majalisar, kuma tuni shugabannin majalisar suka yi Allah-wadai da hakan.

'Yan majalisar dattawan sun yi wani taro na sirri inda suka tattauna lamarin, kafin daga bisani su dawo su ci gaba da zamansu kamar yadda suka tsara.

Wannan layi ne

Mece ce Sandar Majalisa?

  • Sandar Majalisa da ake kira 'Mace' ta sha bamban da sauran alamun majalisar
  • Sandar tana da matukar muhimmancin gaske, inda majalisa ba za ta taba zama ba sai da ita
  • Sandar ita ce alamar iko a dukkan majalisun dokokin kasar na tarayya da na jihohi
  • Ana tafiya da Sandar a gaban shugaban majalisa a duk lokacin da zai shiga ko fita daga majalisar
  • Wani Sajan na Majalisar ne yake da alhakin daukarta a kafadarsa ta dama.
Wannan layi ne

Wane ne Sanata Ovie Omo-Agege

Omo

Asalin hoton, Senate

Bayanan hoto, Sanata Momo Agege
  • Sanata ne mai wakiltar Jihar Delta ta Tsakiya
  • Shekararsa 54
  • An dakatar da shi daga majalisar a makon da ya gabata saboda ya nuna adawa da sauya fasalin dokar zabe
  • Ya ci zabe karkashin jam'iyyar Labour LP
  • Ya taba aiki da hukumar 'yan sanda a shekarar 1987 zuwa 1988
  • Ya taba zama sakataren gwamnatin jihar Delta a 2007
Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so ku karanta: