An tura dakaru na musamman Zamfara

Asalin hoton, Nigerian Air Force
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta aike da dakaru na musamman zuwa Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Rundunar ta ce an dauki wannan mataki ne a kokarin da jami'an tsaro ke yi na dakile ayyukan barayin shanu masu hallaka jama'a.
A kwanakin baya ne 'yan ta'adda suka kaddamar da hare-hare a kauyukan karamar hukumar Anka lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama.

Asalin hoton, Nigeria Air Force
Sai dai wata hira da BBC babban hafsan dakarun sojin saman Najeriya, Air Mashal Sadique Abubakar ya ce an samar da horo ga dakarun da aka tura.
Ya ce nan gaba kadan za'a sake tura karin wadansu dakaru zuwa jihar Zamfara don tunkarar barayin shanu masu hallaka jama'a.
Air Mashal Sadique Abubakar ya ce sojojin kasar za su ci gaba da ba da gudummuwa wajen ganin an kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar Zamfara.







