Mahara sun kashe sama da mutum '1000 a Zamfara cikin shekara shida'

An kashe mutane 'babu adadi'

Asalin hoton, zamfara government

Kisan da mutanen da ake zargi barayin shanu ne suka yi wa wasu mutane a Zamfara da ke arewacin Najeriya ya kara yawan alkaluman mutanen da aka kashe a jihar cikin shekara biyar da suka wuce.

A farkon makon nan ne 'yan bindigar da ake zargi barayin shanu ne suka kashe mutane 35 a harin da suka kai a kauyen Birane cikin karamar hukumar Zurmi.

Sai dai ba wannan ne karon farko da ake kai irin wadannan hare-hare ba.

Hukumomi sun ce suna daukar matakai kan batun, amma masu sharhi kan sha'anin tsaro da ma 'yan kasar na ganin matakan da ake dauka ba su yi tasirin hana kai hare-haren ba.

A watan jiya dan majalisar dattawan da ke wakiltar jihar Zamfara Sanata Kabiru Marafa ya shaida wa BBC cewa masu satar shanu sun kashe kusan mutum 1400 a jihar ta Zamfara cikin shekara biyar.

Sai dai Kwamishinan kananan hukumomin jihar, Alhaji Bello Dankande, ya gaya wa BBC cewa kalaman dan majalisar ya yi na cike da kura kurai.

Ga wasu hare-haren da ake zargi barayin shanu sun kai a jihar ta Zamfara:

Yuni, 2012

Wasu mutane dauke bindigogi sun kashe mutane akalla 23 lokacin suka kai harin kan kauyukan Dangulbi da sabuwar kasuwa Guru da sanyin safiya.

Mutane bakwai ne suka jikkata bayan maharan da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun afkawa kauyukan.

Ana dai jin cewar harin na ramuwar gayya ne kan yadda aka ce 'yan banga a kauyukan suna fatattakar 'yan fashin da ke addabar yankunan, inda a wasu lokuttan suke karkashe su.

Yuni, 2013

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na cewa, fiye da mutane 40 ne aka kashe a garin Kizara da ke Karamar Hukumar Tsafe da ke Jihar ta Zamfara.

Hukumomi sun ce wasu mutane dauke da makamai da ake zargin 'yan fashi ne ne suka kai harin.

Bayanai sun nuna cewa, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da Basarake, da kuma babban limamin garin.

Kakakin gwamnatin jihar ta Zamfara ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar ta Zamfara na daga cikin wasu manyan jami'ai da suka ziyarci garin domin ganin irin abubuwan da suka auku.

Mazauna yankin sun ce harin yana kama da na ramuwar gayya.

Kauyuka a jihar ta Zamfara da wasu yankuna masu makwabtaka da su na fama da irin wadannan hare hare da ake dangantawa da wasu 'yan fashi dake cewar suna daukar fansar kisan wasu 'yan uwansu da aka kashe.

Gwamna Abdul'aziz

Asalin hoton, PREMIUM TIMES

Bayanan hoto, Gwamna Abdul'aziz Yari ya ce suna bakin kokarinsu

Afrilu, 2014

Hukumomi sun ce 'yan bindiga sun kashe fiye da mutum 120 a harin da su ka kai a kauyen 'Yar-Galadima da ke jihar, sai dai mazauna kauyen sun ce adadin ya kai 150.

Hankulan jama'a ya sun tashi sosai a kauyen, inda mata suka gudu, sai maza kalilan suka rage.

Lamarin ya faru ne lokacin da manoma da wakilan kungiyoyin 'yan banga, daga jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna ke wani taro kan yadda za su bullo ma hare-haren da a ke kai masu.

Yuli, 2014

Wasu da ake zargin Fulani ne sun kashe fiye da mutane 50 tare da jikkata wasu da dama a gundumar Gidandawa da ke karamar Hukumar Maradun.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi wa kauyen kawanya ne da misalin karfe biyar na asuba, kana suka bude wuta ga duk wanda suka gani a lokacin.

Yuli, 2015

Wasu 'yan bindiga wadanda ake kyautata zaton barayin shanu ne sun farwa kauyen Ci-gama da ke karamar hukumar Birnin-Magaji a jihar Zamfara, a yammacin jiya Asabar a inda suka kashe mutane 13.

Wani wanda ya shaida al'amarin ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun yi wa kauyen shigar farar dango suka kuma bude wuta akan jama'a.

Disamba, 2015

Wasu 'yan bindiga sun afka wa kauyen Mashema na karamar hukumar Bungudu inda suka kashe mutane ashirin.

Mazauna yankin, wadanda suka tabbatarwa BBC da aukuwar lamarin, sun kara da cewa mutum daya ya samu raunuka a harin.

Fabrairu, 2016

Wasu mutane da ake zaton masu satar shanu ne suka kai hari a kauyen Kwana da ke jihar Zamfara inda suka kashe mutane 23.

Afrilu, 2016

Rahotanni daga jihar Zamfara a Nigeria na cewa, wasu mahara da ake zargin Fulani ne sun kashe mutum shida a ƙauyen 'Yar-tsaba.

Wasu mazauna kauyen shun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne bayan maharan - wadanda suka je kauyen a kan babura - sun buɗe wuta a kan mutanen lokacin da suke gyara gonakinsu.

Mayu, 2016

An kashe sama da mutum mutum goma ƙauyukan Madaɗa da Ruwan Tofa da ke ƙaramar hukumar Ɗan Sadau sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai.

Wani Basarake a yankin ya shaida mana cewa maharan sun kashe mutum bakwai a Madaɗa, yayin da suka kashe mutum uku a Ruwan Tofa, kana suka jikkata mutum biyu.

Maris, 2016

'Yan bindigar da ake zargi masu satar shanu ne sun hallaka mutane da dama a harin da suka kai kauyen Fanteka da ke jihar.

Jami'an 'yan sanda sun ce kimanin mutane tara ne aka kashe a harin, yayin da wasu mazauna yankin suka ce adadin wadanda aka hallaka ya zarta hakan.

Nuwamba, 2016

'Yan bindiga sun sake kai hari a wasu kauyuka a karamar hukumar Zurmi, inda wasu rahotanni ke cewa sun kashe mutane kimanin 44.

Harin - wanda aka kai da daddare - ya faru ne kwana daya bayan an kashe wasu mutane tare da sace wasu da dama, a wani harin na daban da aka kai a kan wasu kauyuka a yankin.

Wasu rahotanni sun ce kimanin mutane dubu daya ne suka tsere daga kauyukan domin tsira da rayukansu.

Rahotannin sun ce 'yan bindigar sun isa kauyukan Tubali da Daular Moriki ne a kan babura masu yawa, inda suka rika harbin kan-mai-uwa-da-wabi.

Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan an yi garkuwa da sama da mutane 40 da suke kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa.

Nuwamba, 2017

Mutanen da ake zargi masu satar shanu da garkuwa da mutane don neman kudin fansa ne sun hallaka fiye da mutum 50 a garuruwan Faro da Kubi da Shinkafi.

Sarkin Shanun Shinkafi Dakta Sulaiman Shu'aibu ya shaida wa BBC cewa, cikin dare mutanen da ake zargin suka je wani kauye mai suna Tunga Kabau, suka kashe mata 25 da kuma maza tara.

Daga nan ne kuma suka bankawa kauyen wuta.

Bayan nan kuma sun nufi wani kauyen da ake cewa Mallabawa, nan ma suka kashe mutum 19.

"Gaskiya ya kamata gwamnatin jihar Zamfara ta sake damara wajen kawo karshen hare-haren da masu satar shanu ke kai wa wasu kauyukansu," in ji Dakta Sha'aibu.

Su ma mazauna garin Faro da Kubi duk a jihar ta Zamfaran, sun ce kwana biyu sun dan samu sassaucin hare-haren 'yan ta'adda da barayin shanu, da kuma dauki dai-dai da ake musu.

Amma kuma tun daga makon da ya gabata hare-haren sun sake dawowa, kamar yadda suka ce.

Wani mazaunin garin Faro ya shaida wa BBC, cewa barayin shanun sun yi mummunar barna da ta hada da asarar rayuka da kona musu amfanin gona.