Ko kun san garin da kusan kowa ke tallan asuwaki?

Bayanan bidiyo, Yadda mata ke sassaka asuwaki a garin Abokim

Bisa tarihi dai kowanne gari da sana'ar da ya shahara a kai wadda kuma galibi al'umarsa ke dogaro da ita.

A kauyen Abokim da ke karamar hukumar Etung a jihar Cross-River ta kudancin Najeriya, baya ga noma wanda shi ne gadon al'umomin Afirka da dama, jama'ar kauyen, maza da mata manya da yara, babu sana'ar da suke yi kamar ta ferewa da kuma tallan asuwaki ko magogi.

Wakilin BBC Is'haq Khalid wanda ya ziyarci kauyen a kwanakin baya, ya ganewa idanunsa yadda wannan sana'a ke gudana da yadda take samar da aikin yi da kudaden shiga ga mutanen.

Jama'ar garin sun shaida masa cewa yawancin itacen da ake yin aswakin da shi, ana sayo shi ne daga yankin kasar Kamaru mai amfani da harshen Ingilishi.

Sai dai rikicin 'yan aware da gwamnati a kasar Kamarun na barazana ga wannan kasuwanci mai muhimmanci ga al'umomin biyu na kan iyakokin kasashen.

Wasu masu wannan sana'a sun shaida wa BBC cewa har jama'a daga wasu kasashen Afirka musamman Jamhuriyar Benin na zuwa garin domin sarar asuwakin buhu-buhu zuwa kasashensu.

Ba ya ga haka kuma, kusan ana safarar asuwakin zuwa sassan Najeriya daban daban.

Daya daga cikin matan da ke wannan sana'a ta shaida wa wakilinmu cewa tana samun ribar naira 5,000 a kan kowanne buhu daya da ta ke sara 5,000.

Fatan jama'ar wannan yanki dai shi ne, sana'ar tasu ta kara bunkasa domin su samu karin kudin shiga, sannan ita ma Najeriya, ta kasance mai alfahari da fitar da magogi kasashen duniya don bunkasa tattalin arzikinta.