Jiragen yaki sun kashe fararen hula 35 a Nigeria — Amnesty

The Nigerian military has been trying to disrupt fighting between herdsmen and farmers, which has damaged homes like the one seen in this picture

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hare-haren sojin sun lalata gidaje da dama

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta ce hare-haren jiragen yakin Najeriya sun kashe fararen hula 35 a watan Disambar da ya gabata na 2017.

Kungiyar ta ce jiragen yaki sun harba rokoki a kauyukan Lawaru da Dong da Shafaron da Nzuruwei a jihar Adamawa domin dakile fada tsakanin manoma da makiyaya.

A kalla kauyuka takwas ne wadannan hare-haren suka lalata.

Sai da kuma duk da haka ba a samu sauki fada tsakanin makiyaya da manoma ba a jihar Adamawan.

Rikicin manoma da makiyaya ya kashe mutum 168 a jihohin Adamawa da Benue da Ondo da kaduna a wannan watan na Disamba.

Duk da haka, Amnesty ta ce matakin da gwamnatin Najeriya ke dauka "bai isa ba kuma a wasu lokutan yana saba wa doka."

Aikin da sojin saman kasar ta yi ranar 4 ga watan Disamba ya biyo bayan hare-haren da makiyaya suka kai kauyuka biyar bayan an kashe musu mutum 51 a watan Nuwamba.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar sojin sama ta Najeriya, Air Commodore Olatokunbo Adesanya, ya shaida wa kafafen watsa labarai na kasar cewa hare-haren saman da rundunar ta kai na gargadi ne ba da niyyar kisa ba.

Ya kara da cewa hare-haren sun sa mutane sun tsere daga wajen kuma sun samar da tasiri mai kyau.

Amma Amnesty tana kira ga gwamnatin Najeriya da ta fitar da bidiyon yadda ta kai harin.

A shekarar da ta gabata, fada tsakanin makiyaya da manoma ya yi sanadin mutuwar mutum 549 tare da raba dubban mutane da muhallansu a fadin Najeriya.