Obasanjo bai isa ya gaya wa Buhari abin da zai yi ba – Dattijan Arewa

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Tuntubar Juna ta Dattawan yankin Arewacin Najeriya wato Arewa Consultative Forum (ACF), ta mayar wa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo martani kan budaddiyar wasikar da ya yi wa Shugaba Buhari cewa kar ya sake tsayawa takara a 2019.
A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Muhammad Biu, ya fitar, ta ce Shugaba Buhari ne kawai yake da damar yanke shawarar sake tsayawa takararsa a zaben 2019.
Cif Obasanjo dai ya rubuta wasika ce a ranar Litinin inda yake shawartar Shugaba Buhari da cewa kamata ya yi ya je ya huta a 2019 saboda yawan shekarunsa da yanayin lafiyarsa.
Kungiyar ACF ta soki Obasanjo da cewa yana son sanya bakinsa a ko wanne al'amari har da wanda bai shafe shi ba.
Wasikar Cif Obasanjo dai ta jawo ce-ce-ku-ce a kasar tun daga ranar Litinin, al'amarin da yake nuna alamar cewa an bude hanyar fara musayar kalamai kan zaben 2019.








