Buhari ya yi tsufa da sake tsayawa takara – Obasanjo

Wasikar Obasanjo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Obasanjo ya ce Buhari na da rauni a fanni tattalin arziki.

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da cewa ya kamata ya hakura da neman ta-zarce a shekarar 2019, saboda yawan shekaru da yanayin lafiyarsa.

A wata budaddiyar wasika da Obasanjo ya fitar wacce BBC ta samu kwafi, tsohon shugaban kasar ya ce mulkin Najeriya al'amari ne da yake bukatar mutum mai cikakkiyar lafiya wanda kuma shekarunsa ba su ja ba, saboda aiki ne ba dare ba rana.

Obasanjo ya kara da cewa Shugaba Buhari yana bukatar lokacin da zai zauna ya yi tunani, ya murmure ya kuma huta da kyau, ta yadda daga baya zai iya shiga sahun tsofaffin shugabannin Najeriya da suke da gogewa da hikima da basirar da za su dinga bayar da shawarwari don ciyar da kasar gaba.

A wasikar ya kuma tabo yadda rikicin makiyaya da manoma yake daukar wani salo daban, yake kuma kara muni ba tare da gwamnatin tarayya ta dauki wani mataki na magance matsalar ba..

"Kuma abun takaicin shi ne yadda bayan kwana guda da kashe kimanin mutum 73 a jihar Benue sai ga shi wasu gwamnoni da ko sakon jaje ba su aika ba sun goyi bayan Shugaba Buhari ya sake neman tsaywa takara a 2019.

"Bai kamata su yi hakan a wannan lokaci ba, bai kamata a mayar da batun rikicin manoma da makiyaya na zarge-zargen juna ba. Dole ne gwamnati ta jagoranci kawo mafita kan hakan," in ji Obasanjo.

A ganinsa, raunin gwamnati da suka dabaibaiye kasa sun hada da karuwar talauci da tabarbarewar tsaro da tattalin arziki da azurta dangi da abokan arziki da saba doka da wanke ma su laifi, da kuma rashin sanin makamar hadin kan kasa.

Tsohon shugaban ya ce, wadannan dalilan ne suka sa ya yi watsi da jam'iyyarsa ta PDP domin marawa 'yan adawa a zaben da ya gabata, domin a cewarsa yana ganin matakin shi ne ya fi dacewa da Najeriya da ma Afirka baki daya a lokacin.

"Halin da Najeriya ta shiga ne ya sa jama'a suka fito jefa kuri'a domin kawar da dan uwana Jonathan".

Obasanjo da Yakubu Gowon

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamata ya yi Buhari ya shiga sahun tsofaffin shugabannin Najeriya da suke da gogewa da hikima da basirar da za su dinga bayar da shawarwari don ciyar da kasar gaba

Obasanjo ya ce duk da cewa shekaru hudu da suka gabata ya yaga katin jam'iyyarsa ta PDP, tare da fito wa baro-baro ya bayyana yin bankwana da siyasa, amma hakan ba zai sa ya kawar da kai da rashin nuna damuwa ga ci gaban Najeriya da Afirka ba.

Sannan Cif Obasanjo ya ce, tun da farko ya san inda shugaba Buhari ke da rauni, kuma ya taba magana tare da rubutu akai tun kafin 'yan Najeriya su zabe shi.

Kuma ya jefa ma shi kuri'a ne saboda a lokacin ana neman wani zabi sabanin Jonathan.

A cewarsa wannan ne dalilin da ya sa ya rubutawa Shugaba Jonathan wasika mai taken "kafin lokacin ya kure", don ya dauki mataki cikin gaggawa amma kuma ya yi watsi da shawarwarin.

Obasanjo ya ce ya san Buhari tun kafin ya zama shugaban kasa kuma ya taba fada cewa yana da rauni a ilimin fahimtar tattalin arziki, amma ya zata zai iya amfani da kwararru da za su iya taimaka ma sa.

"Na san cewa ba za ka iya bayar da abin da ba ka da wadatar shi ba, kuma tattalin arziki fanni ne da ba ruwan shi da bin umurnin soja", a cewar Obasanjo.

Tsohon shugaban ya ce akwai 'yan Najeriya da dama da za su iya taimakawa a fannin ci gaban tattalin arziki da kuma harakokin kasashen waje.

Sannan ya ce akwai manyan zarge-zargen da ake game da wadansu da sai abin suke so ake yi a fadar shugaban kasa da ya kamata ace tuntuni an dauki mataki akai.

"Wannan ai yana iya zama rashawa" in ji Obasanjo.

Tsohon shugaban na Najeriya ya kuma ce kin yin watsi da irin wannan al'ada tare da kawar da kai, tamkar rufa-rufa ne, maimakon gyara. Kuma tabbatar da adalci ya shafi aiki da hannu masu tsabta.

"Na san cewa shugaba Buhari zai yaki rashawa da tayar da kayar baya, kuma dole a yaba ma sa a ci gaban da ya samu a wadannan fannonin guda biyu, amma fa har yanzu da sauran aiki".

Cif Obasanjo ya ce yadda aka bari rikicin makiyaya da manoma ke kara girma ba tare da neman mafita ba, baraka ce ga gwamnatin Tarayya.

Ya ce wani abin bakin-ciki shi ne, yadda wasu gwamnoni suka fito suna yi wa Buhari kamfen, a yayin da a Benue ake zaman makokin binne gawarwakin mutane 73 da aka kashe amma ba tare da gwamnonin sun aika da sakon ta'aziya ba.

Tsohon shugaban ya ce gwamnatin tarayya ce ya kamata ta zauna ta samar da mafita ga rikicin makiyaya da manoma domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Obasanjo ya zana abubuwa uku game da gwamnatin Buhari.

1.Gwamnatin 'yan uwa da abokan arziki, da rashin daukar mataki a kan gurbatattu a fadar shugaban kasa.

2.Rashin fahimtar siyasar cikin gida.

3.Daura laifin gazarar gwamnati a kan gwamnatocin da suka gabata.